Sauya sheka: Majalisar dokokin jihar Oyo ta fara shirin tsige mataimakin gwamna

Sauya sheka: Majalisar dokokin jihar Oyo ta fara shirin tsige mataimakin gwamna

  • Bayan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, majalisar dokokin Oyo ta fara shirin tsige mataimakin gwamna, Rauf Olaniyan
  • Bayan karanta ƙorafi kan mataimakin gwamnan, yan majalisa 24 cikin 32 suka sa hannun don cigaba da bin matakan tsige shi
  • Kakakin majalisar ya ce yanzu sun ba Olaniyan mako guda ya kare kansa kan tuhumar da ake masa ko ya fuskanci rasa kujerarsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Oyo - Majalisar dokokin jihar Oyo ta fara bin matakan tsige mataimakin gwamna, Rauf Olaniyan, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A kwanakin bayan nan ne Olaniyan ya fice daga jam'iyya mai mulkin jihar Oyo PDP zuwa jam'iyyar All Progressive Congress wato APC.

Bayan mataimakin gwamnan ya sauya sheƙa, jam'iyyar PDP ta buƙaci ya gaggauta yin murabus daga kujerarsa ko kuma ya shirya za'a tsige shi.

Kara karanta wannan

2023: PDP na tsaka da kokarin zaɓo mataimakin Atiku, Sanata mai ci ya sauya sheƙa zuwa APC a hukumance

Mataimakin gwamnan Oyo, Rauf Olaniyan.
Sauya sheka: Majalisar dokokin jihar Oyo ta fara shirin tsige mataimakin gwamna Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Shirin da majalisa ta fara ta tsige shi

Mambobi 24 cikin 32 da ke majalisar dokokin sun rattaɓa hannu a korafi kan mataimakin gwamnan, wanda kakakin majalisa ya karanta a zaman yau Laraba. 15 ga watan Yuni, 2022.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ƙorafin, an tuhumi mataimakin gwamnan da rashin ɗa'a, cin mutuncin ofis, rashin zuwa ofis da gudanar da ayyukan ofishin mataimakin gwamna, rashin kunya da sauran su.

Kakakin majalisar dokokin, Adebo Ogundoyin, ya ce ƙorafin ya cika sharaɗin kaso biyu cikin uku na majalisa domin fara bin matakan tsige wa.

Ya ƙara da cewa majalisa ta bai wa mataimakin gwamnan kwanaki Bakwai ya kare kansa kan tuhume-tuhumen da ake masa. Kwanakin zasu kare ranar 22 ga watan Yuni.

Kakakin ya ƙara da cewa rashin zuwa ya kare kansa zai jawo fara shirin tsige shi daga kujerarsa gadan-gadan ba tare da ɓata lokaci ba, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan takarar shugaban ƙasa ya fice daga jam'iyya bayan shan kaye a zaɓen fidda gwani

A wani labarin kuma Sanatan Oyo ya yi murabus daga jam'iyyar PDP, ya koma APC a hukumance

Sanata mai wakiltar kudancin jihar Oyo, Sanata Kola Balogun, ya tabbatar da sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC a hukumance.

Sanatan ya aike da wasikar matakin da ya ɗauka ga shugaban majalisar dattawa kuma ya karanta a zaman su na ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262