2023: Tikitin Musulmi da Musulunmi haramun ne a Addinin Musulunci, Sheikh Maraya

2023: Tikitin Musulmi da Musulunmi haramun ne a Addinin Musulunci, Sheikh Maraya

  • Sheikh Halliru Maraya ya ce haɗa dan takara da mataimaki duk musulmai ya saɓa wa Addinin musulunci
  • A cewar Malamin, Musulunci ya na son yi wa kowane addini adalci da kuma ganin an kyautata musu
  • A cewarsa duk ƙasar da ta haɗa addinai a cikinta, to ya kamata a jawo kowane addini wajen tafiyar da harkokin mulki

Kaduna - Babban Malamin addinin Musulinci a arewacin Najeriya ya ce haɗa ɗan takara da mataimaki masu addini ɗaya a ƙasa mai al'umma Musulmi da Kirista ya saɓa wa ƙa'idojin musulunci.

Sheikh Halluru Maraya, a wata fira da BBC Hausa, ya ce idan har adalci ake son yi wajen tafiyar da mulkin ƙasa to dole a jawo kowane addini.

Babban Malamin kuma tsohon mai ba da shawara kan harkokin addinin Islama na jihar Kaduna, ya ce matuƙar ana son nasara a kowane irin jagoranci to sai an yi adalci.

Kara karanta wannan

2023: PDP na tsaka da kokarin zaɓo mataimakin Atiku, Sanata mai ci ya sauya sheƙa zuwa APC a hukumance

Sheikh Halliru Maraya.
2023: Tikitin Musulmi da Musulunmi haramun ne a Addinin Musulunci, Sheikh Maraya Hoto: Tijjaniya Group/facebook
Asali: Facebook

A kalamansa Shehin Malamin ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Musulunci addini ne da ko wane lokaci ya ke son a yi wa mabiya sauran Addinai adalci kuma a kyautata zama da su, hakan na nufin a bai wa kowane mai haƙƙi hakkinsa ba tare da tauye masa ba."
"Najeriya ƙasa ce ta mabiya Addinin Musulunci da waɗan da ba Musulmai ba, bisa haka wajibi kirista ya yi wa musulmi Adalci, shi ma musulmi ya yi wa kirista adalci"

Bugu da ƙari babban Shehin Malamin ya kara da cewa Musulunci ya umarci yi wa kowa adalci da ba shi haƙƙinsa a matakin jagorancin al'umma.

Saboda haka ya dace a ƙasa kamar Najeriya a tafiyar da shugabanci ta yadda ba wanda zai ce an ware shi, inji Maraya.

Shin me ya kamata a yi?

A cewar Halliru maraya ya kamata a yi wa kowa adalci tun a wurin neman mulki, bai kamata wani Addini ya babbake komai shi kaɗai ba.

Kara karanta wannan

Kannywood: Jaruma Hadiza Gabon ta gurfana a gaban Kotun Musulinci kan tuhumar yaudarar aure

Wannan na zuwa ne yayin da APC ke faɗi tashin zakulo wani Musulmi a arewa ya zama mataimakin ɗan takararta, Bola Tinubu, wanda shi ma musulmi ne.

A ganin Malam Maraya duk lokacin da aka tsayar da kirista takara, to kamata ya yi mataimakinsa ya zama daga wani addini daban, haka idan Musulmi aka tsayar.

"Idan masu addini ɗaya suna shugabancin ƙasa irin Najeriya, ɗayan zai ga cewa ba a masa adalci ba, kuma hakan ka iya haifar da rasa rayuka da dukiyoyi."

A wani labarin kuma gwamna Matawalle ya ce baki ɗaya baƙin auren da yan bindiga suka sace zasu kuɓuta da ikon Allah

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci iyalan mutanen da aka sace su kwantar da hankulan su, yan uwansu zasu kubuta.

Gwamnan ya nuna damuwarsa da ƙara taɓarɓarewar tsaro a jihar, inda ya ce gwamnatinsa ba zata runtsa ba sai mutane sun zauna lafiya.

Kara karanta wannan

Aikin Allah: Bidiyon yadda wani mutumi ya shiga ya tuƙa Tankar Fetur mai ci da wuta don ya ceci mutane

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262