Yanzu-Yanzu: Atiku ya shiga ganawa da Gwamnonin PDP kan zabo abokin takararsa
- Dan takarar jam'iyyar PDP na shugaban kasa ya gana da gwamnonin PDP kan batun zabo abokin gaminsa na 2023
- Atiku Abubakar, na daga cikin wadanda za su gwabza a zaben 2023 mai zuwa, bayan lashe zaben fidda gwani
- Ya zuwa yanzu, ba a san sakamakon ganawar ba, kasancewar batutuwa ba su fara fitowa a kai ba tukuna
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya shirya wani taron tattaunawa da gwamnonin da aka zaba a dandalin jam’iyyar PDP na kasar nan.
Taron wanda aka fara a baya kadan, an shirya shi ne domin kawo karshen shirin zabar wanda zai tsaya takara tare da Atiku.
Jaridar Vanguard ta ce ta samu sanarwar taron da Sakatariyar kungiyar Gwamnonin PDP ta fitar, wanda ke dauke da sa hannun Darakta-Janar na PDP GF, CID Maduagbanam.
A cewar sanarwar za a fara taron ne a Legacy House da ke Abuja da karfe 2:30 na rana, inji Daily Post.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A jiya, Talata, shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyiochia Ayu, da mambobin kwamitin da aka kafa domin zabo abokin gamin Atiku, sun gana kan wannan batu.
An tattaro cewa Atiku baya wurin taron, amma zai gana da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar, wanda shi dai taron da ke gudana ake kyautata zaton shi ne.
A taron da aka yi jiya, Ayu ya ce jam’iyyar za ta bayyana abokin gamin takarar Atiku cikin sa’o’i 48.
Idan dai za a iya tunawa, bayan kammala zaben fidda gwani, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bai wa jam’iyyu har zuwa ranar Juma’a da su mika sunayen ‘yan takararsu na shugaban kasa da kuma abokan takararsu.
Shirin 2023: PDP ta yi watsi da batun zaban Wike a matsayin abokin takarar Atiku
A wani labarin, babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi watsi da rade-radin da ake yi cewa kwamitinta ya zabi gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar.
Vanguard ta ruwaito cewa, kwamitin zaben na jam’iyyar PDP, ya yi taro a jiya, domin cika aikin da ya rataya a wuyansa na ba da shawarar kan abokin tafiyar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubakar.
Da yake magana kan wannan lamari a Abuja, Laraba, Sakataren Yada Labarai na kasa na PDP, Debo Ologunagba, ya ce rahotannin da ake yadawa a kafafen yada labarai na cewa PDP ta zabi Wike kawai jita-jita ne.
Asali: Legit.ng