Musulmi da Musulmi: Yan Najeriya basu damu da addinin yan takara ba – Baba Ahmed
- Kakakin kungiyar dattawan arewa, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya ce yan siyasa na buga wasa da imani, makoma da kuma tunanin yan Najeriya
- Da yake martani kan tikitin takara na Musulmi da Musulmi, Baba-Ahmed ya ce a duk sanda lokacin zabe ya zo, sai yan siyasa su dunga amfani da addini wajen darewa kujerar mulki
- Sai dai kuma ya ce yan Najeriya sun waye a yanzu, inda yace talakawa sun daina damuwa da addinin shugabanninsu
Kakakin kungiyar dattawan arewa, Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa a yanzu talakawan Najeriya basu damu da addinin shugabannin siyasarsu ba.
Daily Trust ta rahoto cewa Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 14 ga watan Yuni, yayin wata hira da gidan talbijin na Channels.
A yan kwanakin nan, ana ta cece-kuce a kasar kan addinin yan takarar shugaban kasa da kuma wadanda za su tsayar a matsayin abokan takararsu.
Tunda yan takarar manyan jam’iyyun siyasar kasar guda biyu wato All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) musulmai ne, mutane da dama ciki harda kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) ta nemi abokan takararsu su kasance kiristoci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da aka nemi ya yi martani kan lamarin na tsayar da Musulmi da Musulmi, kakakin kungiyar dattawan na arewa ya ce addini kambu ne da yan siyasa ke amfani da shi don darewa kujerar mulki a 2023, yana mai cewa bin tsarin addini wajen zabar shugabanni bai tsinanawa yan Najeriya komai ba.
Jaridar The Cable ta nakalto yana cewa:
“Ina ganin akwai yaudara da yawa a nan wanda ya taru yayin da ‘yan siyasa suka fara kara koyo ilimi game da raunin talakawan Najeriya. Mafi yawanmu kashi 90 cikin 100 a matsayinmu na Talakawan Najeriya Kiristoci da Musulmai ne. Muna ba addininmu kula sosai. Mun damu da arzikin imaninmu. Ba ma son a kawo mana hari ko kuma abu ya shafe mu saboda mu Kiristoci ne ko Musulmai.
Mataimakin shugaban kasa: Daga karshe Tinubu ya fayyace gaskiyar lamari kan tikitin Musulmi da Musulmi
“Gaba daya, a lokuta da dama, addininmu addini ce. 'Yan siyasa suna amfani da addini da sauran nau'o'in siyasa wajen darewa kujerar mulki. Wannan shi ne gaskiyar lamari kuma yana kara fitowa fili cewa duk lokacin da siyasa ta zo, addini yana bayyana a matsayin hujja kuma abin da yake yi shi ne ya haifar da wannan ra'ayin cewa 'yan Najeriya za su yaki juna saboda mataimakin shugaban kasa ba Kirista ko Musulmi ba ne.
“Ba za mu yi ba. Ba za mu yi fada ba saboda idan kuka duba tarihi, babu wani abu guda daya da kirista ya amfana da shi daga lokacin da kiristoci ke shugabanci ko mataimakan shugaban kasa. Babu abun da musulmi ya amfana da shi daga lokacin da shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa yake Musulmi.
“Idan kuka ji su suna magana a yanzu, kamar dai shine babban abun kasancewa Musulmi ko Kirista. Idan wanda kake kira mutuminka baya kan shugabanci. Wannan shirme ne. wannan shine babban yaudara da yan siyasa ke yi. Wani abin da ya fi cutarwa shi ne yadda suke kara tabarbarar da abun a yanzu daidai lokacin da ake bukatar samun shugabanci nagari, mutanen kirki ba tare da la’akari da addininsu ba, wadanda za su yi mulkin kasar nan sannan su fitar da ita daga wannan kuncin da muke ciki.
“Yan siyasa na kawo duk wadannan abubuwan da nufin ba yan kadan daga cikinsu fifiko. Yanzu, ka ji wadannan mutanen da cewa dole ya kasance tikitin Musulmi da Musulmi, talakawan Najeriya basu damu ba. Yan siyasa na buga wasa da addini, tunani da makomar goben mutanenmu.
“Ina mai fada maku talakawan Najeriya basa la’akari da addinin shugabanninsu a yanzu. Mun koyi darusa masu nuni daga shugabanninmu na baya wadanda ta iya yiwuwa sun amfana da siyasar addini amma suka yi watsi da mutanen da suke kan tafarkin addini daya. Ina ganin mutane sun waye a yanzu.”
Tikitin Musulmi-Musulmi: Kiristoci na da kariya saboda matar Tinubu fasto ce, inji Orji Kalu
A gefe guda, shugaban masu tsawatarwa a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Orji Uzor Kalu, ya tsoma baki a cece-kuce da ake ta yi kan batun tsayar da dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa daga addini guda.
Babban karramawar da za a yiwa jaruman damokradiyya shine fatattakar APC daga mulki – Atiku Abubakar
Ana dai ta kai ruwa rana tun bayan da alamu suka nuna jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki na iya tsayar da Musulmi da Musulmi a matsayin yan takararta na kujerar shugabancin kasar.
Yayin da kungiyar kiristocin Najeriya ta yi watsi da shawarar sannan ta gargadi jam’iyyu a kan haka, wasu masu ruwa da tsaki sun bukaci yan Najeriya da su mayar da hankali kan cancanta fiye da akida.
Asali: Legit.ng