Yanzu-Yanzu: Shugaban PDP, Tambuwal da wasu jiga-jigan jam'iyya sun sa labule kan mataimakin Atiku

Yanzu-Yanzu: Shugaban PDP, Tambuwal da wasu jiga-jigan jam'iyya sun sa labule kan mataimakin Atiku

  • Yanzu haka ƙusoshin jam'iyyar PDP sun shiga ganawar sirri a babbar Sakatariyar Abuja kan wanda zai zama mataimakin Atiku
  • Shugaban PDP na ƙasa, Sanata Ayu, Gwamna Tambuwal, da sauran jiga-jigan jam'iyya sun hallara kuma sun fara taron yanzun nan
  • Hukumar INEC ta ba jam'iyyun siyasa wa'adi daga nan zuwa 17 ga watan Yuni, su miƙa mata sunayen yan takarar shugaban kasa da mataimaka

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban babbar jam'iyyar hamayya wato PDP, Iyiochia Ayu, da sauran mambobin kwamitin da aka kafa don zakulo mataimakin ɗan takarar shugaban kasa, yanzu haka sun shiga ganawar sirri a Abuja.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa yanzun nan manyan jiga-jigan suka fara gudanar da taron a babbar Sakatariyar PDP dake babban birnin tarayya, Abuja.

Dan takarar PDP, Atiku Abubakar.
Yanzu-Yanzu: Shugaban PDP, Tambuwal da wasu jiga-jigan jam'iyya sun sa labule kan mataimakin Atiku Hoto: @officialPDPNig
Asali: Facebook

Rahoto ya nuna cewa sun fara taron ne domin zaƙulo mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, wanda yan Najeriya zasu amince da shi.

Kara karanta wannan

2023: Sabbin bayanai masu ƙarfi kan wanda PDP ke shirin bayyana wa a matsayin mataimakin Atiku

Mahalarta taron sun haɗa da shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, gwamnan Bauchi, Bala Muhammed, da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauran su ne; tsohon gwamnan Ondo, Olusegun Mimiko, tsohon gwamnan Kuros Riba, Liyel Imoke, Sanata Philip Aduda, da dai sauran su.

Yaushe wa'adin da INEC ta ba jam'iyyu ke ƙarewa?

Idan baku mance ba, bayan kammala zaɓen fidda gwani, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta sanya wa jam'iyyun siyasa wa'adin miƙa mata sunayen yan takara.

INEC ta bai wa jam'iyyun siyasar ƙasar nan wa'adin ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni, 2022 kowace jam'iyya ta tabbatar da ta miƙa sunan ɗan takarar shugaban kasa da mataimaki.

Haka zalika, INEC ta ba jam'iyyun wa'adi zuwa ranar 15 ga watan Yuli su kai mata sunayen yan takarar gwamnoni da mataimakansu, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Shugaba Buhari ya sa labule da gwamnoni 7 na APC kan zaɓen mataimakin Tinubu

A wani labarin kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa ya fice daga jam'iyya bayan shan kaye a zaɓen fidda gwani

Tsohon mataimakin gwamnan CBN, Kingsley Moghalu , ya fice daga jam'iyyar ADC bayan rashin samun tikitin takara.

Moghalu, a wata takarda da ya aike wa shugaban ADC, ya ce rashin adalcin da aka yi a zaɓen fidda gwani ne ya sa ya ɗauki wannan matakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262