Shugabannin Majalisar Dattawa biyu sun yi murabus daga kan muƙamansu a hukumance

Shugabannin Majalisar Dattawa biyu sun yi murabus daga kan muƙamansu a hukumance

  • Bayan sauya sheƙa, Sanata Abaribe, da Sanata Yahaya Abdullahi sun yi murabus daga kujerunsu na majalisar Dattawa a hukumance
  • Abaribe, shugaban marasa rinjaye na majalisa ya koma APGA daga PDP, yayin da shugaban masu rinjaye, Sanata Abdullahi, ya koma PDP daga APC
  • Sanata Ahmad Lawan ne ya sanar da matakin sanatocin a zaman yau Talata bayan dawowa daga hutu

Abuja - Sanata Enyinnaya Abaribe da takwaransa, Sanata Yahaya Abdullahi, sun yi murabus daga kan kujerunsu na shugaban marasa rinjaye da shugaban masu rinjaye na majalisar Dattawa a hukumance.

Shugaban majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, shi ne ya sanar da haka yayin karanta wasikun murabus ɗin su a zauren majalisa bayan dawowa daga hutu ranar Talata.

Daily Trust ta ruwaito cewa shugabannin majalisar biyu sun yi murabus ne biyo bayan sauya shekar da suka yi daga jam'iyyun da mutane suka zaɓe su har suka ɗare kujarar Sanata.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Shugaban PDP, Tambuwal da wasu jiga-jigai sun sa labule kan mataimakin Atiku

Sanata Abaribe da Sanata Yahaya Abdullahi.
Shugabannin Majalisar Dattawa biyu sun yi murabus daga kan muƙamansa a hukumance Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Abdullahi da Abaribe sun samu saɓani da jam'iyyun ne har ta kai ga suka sauya sheƙa zuwa wata jam'iyya sakamakon gaza samun tikitin tazarce kan kujerun su a zaɓen 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da Abaribe ya fice daga jam'iyyar PDP kuma ya koma jam'iyyar APGA, shi kuma Sanata Abdullahi ya sauya sheƙa ne daga APC zuwa PDP.

Shugaban majalisa, Sanata Lawan ya ce:

"Sanata Enyinnaya Abaribe ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APGA, haka nan kuma ya yi murabus daga kujerar shugaban marasa rinjaye. Saboda haka kujerar ta zama bakowa domin PDP ta cike gurbin."
"Ina yi wa takwaran mu Sanata Abaribe fatan Alkairi da nasara a sabuwar jam'iyyarsa APGA. Muna da mutum ɗaya da ke wakiltar APGA a majalisa kamar YPP."

Dalilin da yasa na bar APC - Sanata Abdullahi

A wasiƙar murabus ɗinsa, Sanata Yahaya Abdullahi, ya ce ya tattara kayansa daga APC ne saboda rashin demokaraɗiyya a cikin gida, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abokin takara: Atiku na daf da daukar Gwamna mai-ci, Tinubu zai tafi da tsohon Gwamna

Ya ce gwamna ya babbake komai na jam'iyyar reshen jihar Kebbi kuma uwar jam'iyya ta kasa ta gaza warware rikicin da ya addabi reshenta na jihar.

"Ba zan cigaba da aiki ga gwamnati a asalin cibiya ba yayin da mutane na ke fama da baƙin talauci. Bayan gaza samun adalci a APC na koma jam'iyyar PDP."

A wani labarin kuma Shugaban PDP, Tambuwal da wasu jiga-jigan jam'iyya sun sa labule kan mataimakin Atiku

Yanzu haka ƙusoshin jam'iyyar PDP sun shiga ganawar sirri a babbar Sakatariyar Abuja kan wanda zai zama mataimakin Atiku.

Shugaban PDP na ƙasa, Sanata Ayu, Gwamna Tambuwal, da sauran jiga-jigan jam'iyy sun hallara kuma sun fara taron yanzu nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262