Ciki ya duri ruwa: Mun ji tsoron Bola Tinubu ya samu takara a APC inji ‘Dan takaran PDP

Ciki ya duri ruwa: Mun ji tsoron Bola Tinubu ya samu takara a APC inji ‘Dan takaran PDP

  • Farfesa Sandy Ono ya fito karara ya nuna jam’iyyar PDP ta na jin tsoron Asiwaju Bola Tinubu a 2023
  • Ono wanda yake rike da tutar PDP a jihar Kuros Riba ya ce ba su ji dadi Tinubu ya samu takara ba
  • Sanatan ya na ganin sai PDP da Atiku Abubakar sun yi da gaske sannan za a hana APC yin nasara

Cross River - ‘Dan takarar kujerar gwamna a jihar Kuros Riba, Sandy Onor ya ce an shiga halin dar-dar a PDP a kan yiwuwar takarar Asiwaju Bola Tinubu.

Farfesa Sandy Onor ya nuna cewa jam’iyyar PDP ta ji tsoron APC ta tsaida Asiwaju Bola Tinubu a 2023. Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen tsoffin masu takara da Tinubu ya ziyarta tun bayan da ya mallaki tutar APC

A karshe kuwa Bola Tinubu ya samu tutar jam’iyyar mai mulki da gagarumar nasara. Tsohon gwamnan ya samu kuri’a 1271, ya doke abokan takararsa 13.

Sandy Onor wanda shi ne Sanatan Kuros Riba ta tsakiya a majalisar dattawa ya shaidawa ‘yan jaridar cewa ba su so Tinubu ya zama ‘dan takaran APC ba.

Da yake jawabi a gaban manema labarai a garin Kalaba a karshen makon da ya wuce, Onor ya nuna takarar Tinubu za ta iya zama babbar barazana ga PDP.

Sanatan mai-ci yake cewa Tinubu zai kawo masu matsala a zaben shugaban kasan da za ayi a 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bola Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu Hoto: officialasiwajubat
Asali: Facebook

A cewar Farfesan, ya zama dole jam’iyyar hamayya ta PDP ta hada-kai domin ganin ta doke APC a zaben 2023 da nufin a kawowa al’ummar kasar nan cigaba.

Kara karanta wannan

Atiku zai nemi hadin-kan Kwankwaso da Obi a 2023, APC na lissafin abokin takaran Tinubu

Ba haka aka so ba, amma ...

“Samun takarar tsohon Gwamnan Legas, Alhaji Bola Tinubu, abu ne ba mu yi tsammani ba. Ba mu so hakan ta faru ba.”

- Farfesa Sandy Onor

Amma duk da haka, ‘dan takaran na 2023 yana ganin kar-ta-san-kar domin tun da PDP ta tsaida Atiku Abubakar, jam’iyyar za ta iya tunkarar APC mai mulki.

Onor yana ganin Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar zai iya kawo karshen gwamnatin APC.

A jawabin na sa, Sanata Onor yace wani abin da zai yi tasiri a zaben 2023 shi ne wadanda aka dauko su yi takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a badi.

Yaran da Tinubu ya kawo

Idan aka bi tarihi, za a samu labari akwai mutane birjik da suka ci albarkacin Bola Tinubu, suka samu kujeru a gwamnati da mukamai a siyasa saboda shi.

Akwai Gwamnonin jihohi da ‘Yan Majalisa da a sanadiyyar Bola Tinubu suka dare mulki. Shi ne silar zaman Yemi Osinbajo mataimakin shugaban kasa a 2015.

Kara karanta wannan

Barazana da kalubale 8 da Bola Tinubu ya fuskanta wajen zama ‘Dan takaran APC a 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng