2023: CAN ta Aike Sako ga Masu Neman Shugabancin Kasa, Ta Sanar da Irin 'Dan Takarar da Zata Zaba
- Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ta yi kira ga 'yan takarar shugabancin kasa da kada su ware coci a gefe
- CAN ta sanar da cewa, duk 'dan takarar da ke son ya kai labari a zaben 2023, dole ne ya hada kai da cocinan kasar nan
- Ta ja kunnen 'yan takarar kan yin tikitin Musulmi da Musulmi, don ta ce babu daidaito da adalci a ciki
FCT, Abuja - Kungiyar Kiristoci ta Kasa, CAN, ta ce duk jam'iyyar siyasa da ke son cin zaben shugabancin kasa a 2023 dole ne ta hada kai da coci.
Samson Ayokunle, shugaban CAN, ya sanar da hakan a ranar Lahadi yayin jawabin bikin ranar damokaradiyya na 2022 wanda aka yi a Cibiyar Kiristoci ta Kasa da ke Abuja, The Cable ta ruwaito.
Ayokunle wanda ya samu wakilcin Wale-Oke, shugaban Pentecostal Fellowship of Nigeria, ya ce duk jam'iyyar da ke son samar da shugaban kasa na gaba dole ne ta hada kai da yankunan Kiristoci.
"Yayin da nake taya 'yan takarar murna, dole ne in aike da wannan jan kunnen. Don Allah, kada ku yi tikitin Musulmi da Musulmi. Ba zai tafi ba kuma ba zai tsayu ba. A maimako, zai iya hada fada a kasar nan," yace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Dan takarar da zai ci shi ne wanda ya yi aiki tare da coci. Don Allah kada ku ware coci.
"Idan kun rungumi daidaito da adalci, masu zaben Najeriya za su saka muku da kuri'u kuma za su ba ku goyon baya."
Shugaban CAN ya kara da cewa, kasar nan ba za ta yi ikirarin tabbatar da adalci ba in har aka dakile wani yanki daga samar da shugaban kasa.
"Zaku iya mulki ne in har akwai kasar. A halin neman zaben ku, ku tabbatar kun saka adalci da daidaito. Idan babu kyautatawa, adalci da daidaito, za mu kasance kan mu a rabe," yace.
"Babu adalci idan mutane daga wata kabila aka mayar da su marasa muhimmanci, wadanda ba za su iya samun ofishi mafi daraja na kasar ba.
"Muna addu'ar ganin karshen kisan mutane da ake yi a wuraren bauta. Muna addu'ar samun kasa mai hadin kai inda adalci da daidaito ya samu wurin zama. Ubangiji ya yi mana albarka baki daya kuma yayi wa Najeriya albarka."
Asali: Legit.ng