Bayan rasa tikitin gaje Buhari, gwamna ya karbe tikitin sanata na APC a hannun kaninsa
- Rahoton da ke iso mu a jihar Ebonyi, ya ce tsohon dan takarar shugaban kasa ya lashe zaben fidda gwanin sanata
- Wanan na zuwa ne jim kadan bayan da sha kaye a zaben fidda gwanin shugaban kasa na jam'iyyar APC
- David Umahi, wanda gwamnan Ebonyi ne ya tsaya takara, inda Tinubu ya lallasa shi a zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa
Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya zama wanda ya lashe zaben fidda gwani na sanataocin APC da aka sake a Ebonyi ta Kudu, SaharaRepoters ta ruwaito.
Kanensa, Cif Austin Umahi ne ya zama wanda ya lashe zaben makonni biyu da suka gabata.
Gwamnan ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC amma Bola Tinubu ya lallasa shi a babban taron jam’iyyar da aka gudanar a Abuja.
Jim kadan bayan ya sha kaye, jam’iyyar ta soke zaben fidda gwani na ‘yan takarar sanata na Ebonyi ta Kudu tare da dage zaben zuwa daren Alhamis 9 ga watan Yuni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An sake gudanar da zaben fidda gwanin dan takarar Sanata na jam’iyyar APC na Ebonyi ta Kudu a karamar hukumar Afikpo ta Arewa, inda Gwamna Umahi ya lashe tikitin jam’iyyar.
Bayan shan kaye, kaninsa ya mayar masa tikitin sanata
Wata majiya ta kusa da Gwamnan ta tabbatar wa jaridar The Nation sabon labarin a Abakaliki, cewa gwamnan ya maye nasarar kanisa ne.
Sai dai, majiyar wadda ta nemi a sakaya sunanta ta yi watsi da rade-radin da ake yi na cewa an sake gudanar da sabon zaben fidda gwanin na mazabar majalisar dattawa.
Ya ce:
“Ba a sake shirya zabe ba, abin da ya faru shi ne sauya ‘yan takarar. Dokar zabe ta ba da umarnin cewa dole ne a gudanar da irin wannan atisayen a wurin da aka fara gudanar da atisayen tare da cikakkiyar amincewar dukkan bangarorin da abin ya shafa."
Bayan shan kaye hannun Tinubu, Tsohon ministan Buhari ya lashe tikitin sanata a APC
A wani labarin, tsohon ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya lashe tikitin takarar Sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta arewa maso yamma a jam'iyyar All Progressive Congress wato APC.
Daily Trust ta ruwaito cewa Akpabio, wanda ya janye wa Bola Tinubu a zaben fidda ɗan takarar shugaban kasa da aka kammala, ya samu nasara ne da kuri'u 478.
Kwamitin APC ya tantance Deleget 512 daga cikin guda 540, inda Sir Joseph Akpan ya samu kuri'a ɗaya, Ekpo Udom, wanda ya lashe zaben farko da aka shirya, ya samu kuri'u Uku, yayin da 11 suka lalace.
Asali: Legit.ng