2023: Bayan Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC, Bola Tinubu Ya Ziyarci Fadar Shugaban Ƙasa
- Bayan lashe zaɓen fidda gwanin APC, tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu, ya kai ziyara fadar shugaban ƙasa
- Tinubu tare da rakiyar gwamnan Legas da shugaban Oando Plc, sun gana da shugaban kasa, Muhammadu Buhari
- Shugaban Buhari ya sha alwashin aiki da dare ba rana don tabbatar da cewa Tinubu ya cika burinsa a 2023
Abuja - Ɗan takarar jam'iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci fadar shugaban ƙasa, Abuja da daren ranar Alhamis.
Daily Trust ta ruwaito cewa Tinubu ya kai ziyaran ne tare da rakiyar gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, da shugabn kamfanin Oando Plc, Mista Wale Tinubu.
Manyan jiga-jigan uku sun gana da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda tuni ya sha alwashin yin aiki ba ji ba gani domin Tinubu ya samu nasara.
A wata wasiƙa da ya aike wa gwamnonin APC, Buhari ya bayyana zaɓen fidda ɗan takarar APC da aka kammala a matsayin ɗaya ɗaga cikin wanda ba za'a manta da su ba a tarihin Demokaraɗiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Punch ta rahoto Shugaban ƙasa ya ce:
"Zaɓen fidda gwanin APC ya gudana cikin kwanciyar hankali kuma Deleget sun zaɓi wanda zai ɗauki tutar jam'iyya a zaɓen 2023. A matsayin mamban APC kuma mai faɗa a ji, na gaskata cewa zamu yi aiki tare don nasarar ɗan takarar mu."
"A shekara 7 nan baya da muka kafa gwamnati mun yi abubuwa da dama, kuma muna da sauran ayyukan da ya kamata mu yi. Ayyukan da APC ta ɗakko ba'a je ko ina ba."
"Muna bukatar mu haɗa kawunan mu domin tabbatar da tafiyar da muka faro ta cigaban zaman lafiya da kwanciyar hankali ta ɗore."
Zamu yi aiki tukuri don nasarar Tinubu - Buhari
Shugaba Buhari ya ƙara da cewa Tinubu ba baƙo bane, kowa ya san shi kuma ya san tarihin nasarar sa, don haka wajibi kowane mamban APC ya goya masa baya.
"Saboda haka yanzu lokaci ya yi da zamu haɗa kai mu tunkari gaba, kamar yadda muka yi a 2015, mu kai APC ga gagarumar nasara. A shirye nake na yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnonin APC don taiamka wa Tinubu ya yi nasara a 2023."
A wani labarin kuma Tsohon dogarin Abacha, Hamza Al-Mustapha, ya lashe zaben fidda ɗan takarar shugaban kasa
Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya lashe zaben fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AA a zaɓen 2023.
Tsohon dogarin Marigayi Janar Sani Abacha, ya samu wannan nasara ne bayan lallasa abokin hamayyarsa da kuri'u 506.
Asali: Legit.ng