Daga karshe, Osinbajo ya taya Tinubu murnar nasara a zabe
- Daga karshe Farfesa Yemi Osinbajo ya taya jagoran APC, Asiwaju Bola Tinubu, murnar nasara a zaben
- Asiwaju Bola Tinubu ya samu gagarumar nasara kan tsohon minista Chibuike Rotimi Amaechi da Osinbajo
- Mutan yankin Yarabawa na tuhumar Osinbajo da wadanda suka mai aiki matsayin mayaudara Tinubu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya taya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, murnar nasara a zaben fidda gwanin yan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC.
Osinbajo ya aike da sakon taya murnarsa ne bayan kwana daya da shan kaye a zaben.
Yace:
"Ina taya Asiwaju Bola AHmed Tinubu murnar nasara a zaben fidda gwnain jam'iyyarmu da zama dan takarar jam'iyyarmu a zaben shugaban kasar 2023."
"Tsawon shekara da shekaru, Tinubu ya nuna kwarewa da jajircewa wajen gina kasa."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Asiwaju Bola Tinubu ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar APC
Tsohon gwamna jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya lashe zaben fidda gwanin yan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC.
A zabensa na farko tun bayan barin mulki a 2007, Tinubu yanzu shine zai wakilci jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa a zaben shekarar 2023.
Tinubu ya lallasa yan takara 12 da suka fafata a zaben inda ya samu kuri'u sama da 1,271
Wanda ya zo na biyu shine tsohon Gwamnan jihar Rivers, kuma tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi wanda ya samu kuri'u 316.
Sannan Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya samu kuri'u 235.
Asali: Legit.ng