2023: Tambuwal Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Gwamnonin PDP Suka Yi Taro Da Atiku

2023: Tambuwal Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Gwamnonin PDP Suka Yi Taro Da Atiku

  • Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto ya yi magana kan ganawar da gwamnonin PDP suka yi da dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar
  • Shugaban kungiyar gwamnonin PDP ya shaida wa manema labarai bayan taron cewa sun yi taron ne don gode wa gwamnoni kan rawar da suka taka yayin zaben fidda gwani kuma ana tuntuba kan batun zaben mataimakin Atiku
  • Atiku ya mika sakon taya murna ga Asiwaju Bola Tinubu bayan an sanar da shi a matsayin wanda ya zama dan takarar shugaban kasar APC a shekarar 2023

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2023, Atiku Abubakar, ya yi ganawar sirri da gwamnoni da aka zaba a karkashin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Yanzu: Atiku Da Gwamnonin PDP Sun Shiga Taron Sirri Bayan Nasarar Tinubu A Zaben Fidda Gwanin APC

Wasu majiyoyi da suke da masaniya kan taron sun shaida wa Vanguard cewa wannan taron shine na farko cikin taruruka da za a yi don shirin kamfen din babban zaben 2023.

Tambuwal Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Gwamnonin PDP Suka Yi Taro Da Atiku
Tambuwal: Dalilin da ya sa gwamnonin PDP suka gana da Atiku. Hoto: @atiku.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a karshen taron, shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal ya ce:

"A madadin takwarori na wato gwamnoni, bari in yaba wa shugabannin jam'iyyar da mambobin jam'iyyar bisa nasarar yin taron mu na kasa.
"Shugaban jam'iyyar na kasa tare da dan takarar sun zo su yi wa gwamnoni godiya bisa rawar da suka taka yayin taron.
"Mun yi magana kan hadin kai wurin ganin mun yi kamfen din zabe da zai samar wa PDP nasara a zabukan da dama daga majalisun wakilan jihohi, zaben kasa, zaben gwamnoni da zaben shugaban kasa a Fabrairun 2023.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban PDP Ya Bayyana Abin Da Yasa Za Su Ci Zaben Shugaban Kasa Da Jihohi Da Dama a Najeriya

"Taro ne na tuntuba kan batutuwan da ke gaban mu."

Da ya ke amsa tambayar da aka masa kan ko an tattauna batun zaben mataimakin dan takarar shugaban kasa na PDP, Tambuwal ya ce:

"Ana tuntuba kan abin, ana cigaba kuma ana tuntubar gwamnoni a kan hakan."

2023: Shugaban PDP Ya Bayyana Abin Da Yasa Za Su Ci Zaben Shugaban Kasa Da Jihohi Da Dama a Najeriya

A wani rahoton, Shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya ce yana kyautata zaton cewa jam'iyyarsa za ta ci zaben shugaban kasa da mafi yawancin jihohin kasar a 2023, rahoton Vanguard.

Ayu ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai bayan mika takardun shaidan cin zabe na wadanda suka yi nasara a zaben fidda gwani na gwamnoni a Abuja, ranar Talata.

Ya ce dalilinsa shine mafi yawancin yan Najeriya sun gaji da rashin iya shugabanci musamman bangaren tattalin arziki da tsaro da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnonin APC suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164