'Yan takarar shugaban kasa 7 da suka janye wa Bola Tinubu a filin taron APC
- Bayan tsayin dare ana kaɗa kuri'u da duk abinda ya biyo baya, kwamitin zaɓe ya sanar da Tinubu a matsayin wanda ya lashe tikitin shugaban kasa
- Wasu yan takara sun sadaukar wa Tinubu da burin su, inda suka janye kuma suka mara masa baya, mun tattaro muku su duka
- A halin yanzun tsohon gwamnan Legas kuma jagoran APC na ƙasa ne zai fafata a zaɓen 2023 karkashin inuwar APC
Abuja - Adadin 'yan takara Bakwai ne suka janye burin su na zama shugaban ƙama kuma suka goyi bayan tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu.
Jam'iyyar APC ta gudanar da zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa a filin Eagle Square da ke babban birnin tarayya Abuja, inda Tinubu ya lashe tikitin da gagarumin rinjaye.
Legit.ng Hausa ta tattaro muku yan takarar 7 waɗan da suka canza shawara kana suka goyi bayan Tinubu a filin taro har ta kai ga ya samu nasara.
Yan takarar da suka janye wa Tinubu
1. Tsohon ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun.
3. Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi.
4. Tsohon kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Dimeji Bankole.
5. Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar Talamiz.
6. Sanata mai wakiltar Ondo ta arewa, Sanata Ajayi Boroffice.
7. Mace ɗaya tilo da ta fito takara, Uju Ohanenye.
Dukkan waɗan nan yan takaran sun sanar da matakin janyewa ne ranar Talata a filin taron APC yayin da aka ba kowane ɗan takara ya gabatar da jawabi.
Bayan kammala ƙirga kuri'u, Bola Tinubu, ya samu nasara da kuri'u 1271, inda ya lallasa tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, wanda ke da kuri'u 316, da Yemi Osinbajo, wanda ya samu 235.
A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya miƙa tutar APC ga ɗan takarar shugaban ƙasa a Abuja
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya damƙa tutar A P C hannun ɗan takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a Abuja.
Babban mai taimaka wa shugaban kan harkokin midiya, Buhari Sallau, ya ce hakan ta faru n e gaban kusoshin jam'iyya yayin rufe taro.
Asali: Legit.ng