2023: Mace Guda Da Ke Takarar Shugaban Kasa a APC Ta Janye Wa Tinubu, Ta Bayyana Dalili
- Uju Ohanenye, mace tilo da ke takarar neman kujerar shugabancin kasa a jam'iyyar APC mai mulki ta janye takararta
- Ohanenye ta janye takarar ne a ranar Talata yayin zaben fidda gwani na APC da ake yi a Abuja ta umurci magoya bayanta su mara wa Bola Tinubu baya
- Yar takarar ta ce ta fahimci lokacin mata bai riga ya zo ba kuma Najeriya na bukatar uwa ta za ta kula da ita don haka za ta zame uwa ga kasa a yanzu
FCT, Abuja - Yar takarar shugaban kasa, Uju Ohanenye, ta janye wa jagoran jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Ta sanar da hakan ne wurin taron jam'iyyar a ranar Talata a birnin tarayya Abuja, The Punch ta rahoto.
Dalilin da yasa Uju ta janye takararta
Ta ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Najeriya na bukatar jagora kuma na yanke shawarar in zama uwar wannan kasar. Najeriya ba ta da kwarewa na mata.
"Na gode muku sosai, amma na lura cewa muna bukatar karin lokaci kafin wannan ya faru. Ina rokon daliget su sani cewa kuri'unsu na ceton rayyuka. Ku yi tunanin iyayenku mata da yaranku kafin ku yi zabe.
"Ku zabi wanda zai tabbatar yayanku za su samu rayuwa mai kyau a gaba. Na ga ya dace in janye wa wannan mai ceton rayukan kuma dan takarar da ya fi kowa cancanta wanda shine Asiwaju Bola Tinubu. Ina rokon magoya baya na su zabi Tinubu."
Yan Takarar Shugaban Kasa A APC Su 7 Sun Ki Yarda Da Sunayen Mutum 5 Da Gwamnoni Suka Mika Wa Buhari
A wani rahoton, wasu daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a APC sun yi watsi da sunayen yan takar da gwamnoni suka mika wa Shugaba Buhari don ya zabi magajinsa daga cikinsu, rahoton Tribune.
Gwamna Bagudu ya bayyana dan takarar da za a kaddamar a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin APC
Wadanda ba su yarda da hakan ba akwai Gwamnan Cross Rivers Ben Ayade; Tsohon Karamin Ministan Ilimi, Emek Nwajiubu; Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, Tsohon gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha da dan kasuwa Tein Jack-Rich.
Shugaban Kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan Jihar Plateau, Simon Lalong ne ya tabbatar da jerin sunayen.
Asali: Legit.ng