Abin da shugaba Buhari ya faɗa wa Deleget a wurin taron APC kafin fara zaɓe
- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gaya wa Deleget irin mutumin da zasu zaɓa ya zama magajinsa a jam'iyyar APC
- A jawabinsa wurin taron APC ranar Talata, Buhari ya roki Deleget da mambobin APC kada su bari PDP ta dawo da Najeriya baya
- A halin yanzun dai Deleget sun kammala kaɗa kuri'un su, kuma nan ba da jimawa ba za'a bayyana wanda ya ci nasara
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya buƙaci Deleget da zasu zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa wanda yake sananne kuma ɗan ƙasa mai bin doka sau da ƙafa, wanda ya yi imani da dunƙulewar Najeriya.
Yayin jawabinsa na wurin taro kafin fara zaɓe, Shugaba Buhari ya nemi Deleget su tabbata sun zaɓi mutum mai ƙwarin guiwar da zai ci da ƙasar nan zuwa mataki na gaba.
Vanguard ta tattaro cewa Buhari ya ƙara da jawo hankalin Deleget da kuma mambobin APC baki ɗaya da cewa ya wajaba a kan su kada su bari PDP ta dawo da ƙasar nan baya.
Ɗan takarar da nake so ku zaɓa - Buhari
A jawabinsa shugaba Buhari ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Ya zama wajibi a akan mu, mu zaɓi wanda mutane suka sani, mai bin dokokin ƙasa sau da ƙafa kuma ya yi amanna da haɗin kan ƙasar nan. Ɗan Najeriya me kwarin guiwar da zai ci da ƙasar mu gaba."
"Bai kamata mu bari jam'iyyar PDP ta dawo kuma ta maida ƙasar nan ta mu baya ba, mu yi aiki tare ba dare ba rana domin jam'iyyar mu ta APC."
Yayin jawabin yan takara, wasu da dama sun sanar da janye wa Bola Tinubu, wasu kuma suka janye wa mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo.
A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya magantu kan kowane ɗaya daga cikin yan takara 5 da gwamnoni suka kai masa
Gwamnan Filato, Simon Lalong, ya ce shugaban ƙasa Buhari ya aminta da dukkan yan takara 5 da muka kai masa gabanin fara zaɓe.
Gwamnan wanda ke jagorantar gwamnonin arewa ya ce ba zai yuwu su tafi wurin zabe da dukkanin yan takara ba.
Asali: Legit.ng