Zaben fidda gwanin APC: Jerin 'yan takara 14 da suka ki janyewa, ake fafatawa dasu
A zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da ke gudana a dandalin Eagle Square da ke Abuja, ‘yan takara 14 ne ke cikin jerin wadanda ake kada wa kuri'u.
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Wasu tara sun janye daga takarar dab lokacin da za a fara kada kuri'u, kamar yadda muka ruwaito a baya.
Janyewar wasu daga cikin 'yan takarar ana sa ran zai kawo wa wasu 'yan takara sauki, kasancewar magoya baya ka iya marawa wanda aka janyewa baya.
A kasa mun tattaro muku jerin sunayen 'yan takarar da suka tsaya tsayin daka sai an fafata dasu, kamar yadda legit.ng ta tattaro.
- Chukwuemeka Uwaezuoke Nwajiuba
- Nweze David Umahi
- Gbolahan B. Bakare
- Ahmed B. Tinubu Ahmad
- Rufai Sani
- Chibuike Rotimi Amaechi
- Yemi Osinbajo
- Rochas Anayo Okorocha
- Yahaya Bello
- Tein Jack-Rich
- Christopher Onu
- Ahmad Lawan
- Ben Ayade
- Ikeobasi Mokelu
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kebbi: Shugaban masu rinjaye a majalisa ya fice daga APC ya koma jam'iyyar PDP
A wani labarin, shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Yahaya Abdullahi ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kebbi, inji Punch.
Mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Muhammad Jamil Gulma, wanda ya tabbatar da sauya shekar ya fitar da sanarwa.
Vanguard ta ruwaito shi yana cewa: “Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Dakta Yahaya Abdullahi a ranar Laraba da karfe 9 na safe zai bar Abuja zuwa Kebbi, ya zarce karamar hukumar Kamba domin shelanta shiga jam’iyyar PDP, kuma zai nuna sha’awar sa ta tsayawa takarar kujerar a yanzu.”
Asali: Legit.ng