Mai Shari'a Ta Kwace Wayoyin Salula Na Yan Jarida Su 6 a Yayin Zaman Kotu Abuja

Mai Shari'a Ta Kwace Wayoyin Salula Na Yan Jarida Su 6 a Yayin Zaman Kotu Abuja

  • Mai shari'a Chizoba Orji ta babban kotun tarayya da ke Abuja ta kwace wayoyin salular wasu yan jarida su 6 yayin zaman kotu
  • Hakan ya faru ne bayan ta shigo kotun ta tarar dan jarida yana cece-kuce da wani ma'aikacin kotu kan daukan hotuna da bidiyo a kotun
  • Daga nan Mai shari'ar ta tsawata wa dan jaridar ta tambaye shi wanda ya bashi izinin daukan hoto da bidiyo a kotunta, daga bisani ta umurci dan sanda mai tsaronta ya kwace wayoyin yan jaridan su shida

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT Abuja - Alkalin babban kotun Abuja ya bada umurnin a kwace wayoyin salular wasun manema labarai su shida a Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Yan jaridan sune Wumi Obabori na AIT; Godwin Tsa Jaridar The Sun; Ikechukwu Nnochiri na Jaridar Vanguard; Austin Okezie na Raypower Fm; Kunle Olasanmi of Jaridar Leadership; and a goggagen dan jarida, Mr. Charles Ozoemena.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sabon rikici ya ɓarke a filin taron APC a Abuja, jami'an tsaro sun fusata

Mai Shari'a Ta Kwace Wayoyin Salula Na Yan Jarida Su 6 a Yayin Zaman Kotu Abuja
Alkaliya Ta Kwace Wayoyin Salula Na Yan Jarida Su 6 a Yayin Zaman Kotu Abuja. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

Mai shari'a Chizoba Orji ta bada umurnin yan jaridar su mika wa dan sandan da ke tsaronta wayoyinsu ne yayin da ta dawo daga hutu ta ga yan jaridar suna jayayya da ma'aikatan kotu kan daukansu hotuna da bidiyo.

Sababin rikici tsakanin yan jarida da ma'aikatan kotun

Daily Trust ta rahoto cewa rikici ya barke ne bayan rajistara na kotun ya dage cewa yan jaridan ba su da ikon daukan hotuna da bidiyo a kotun jim kadan bayan alkaliyar ta tashi ta shiga ofishinta domin shirya yin shari'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan cece-kuce na tsawon awa daya, Mai shari'a Orji ta dawo cikin kotun ta kira dan jaridar AIT ya matso kusa da ita.

"Me yasa ka ke daukan hotuna da bidiyo a kotu na? Wane ya baka izinin yin haka," Alkaliyar ta tambaya.
"Ni dan jarida ne mai daukan rahoto kan shari'a. Mun saba daukan hotuna da bidiyo idan ba zaman sharia ake yi ba, har ma a kotun koli," Obabori ya amsa.

Kara karanta wannan

Zaɓen Magajin Buhari: Yan jaridu sun yi cirko-cirko a kofar shiga Filin taron APC kan abu ɗaya

"Ba ka da ikon yin hakan! Idan an baka izinin yin hakan, a rubuce ya kamata in gani. Wa ya baka izini? Nuna min shaidan da aka baka?" Mai shari'a Orji ta kara da cewa.

A wannan lokacin, sauran yan jaridan da ke kotun suka tashi suka gabatar da kansu.

"Bana son jin komai daga gare ku. Yanzu, ina na'urar da kuka yi amfani da shi wurin daukan hotuna da bidiyon?" Mai shari'a Orji ta tambayi dan jaridar na AIT.

Asali: Legit.ng

Online view pixel