Wata sabuwa: Rikici a APC yayin da ake yunkurin magudi a jerin sunayen deliget
- Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, ana zargin wasu 'yan APC da yunkurin sauya sunayen deliget na zaben fidda gwani
- Rahoton ya yi ikrarin cewa, suna kokarin ganin an samarwa shugaban majalisa, Ahmad Lawan hanya mafi saukin tsallake zaben fidda gwanin
- Sai dai, kunji cewa, har yanzu ana kai ruwa rana a AOPC kan batun da ya shafi shiyya, inda suka ce dole 'yan Kudu su gaji Buhari
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - APC ta dare kan yunkurin da ake yi na yin magudi a jerin sunayen deliget-deliget na zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa.
Jaridar TheCable ta samu labarin cewa akwai wani jerin sunayen da aka sauya da ake son baiwa shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan wanda yana daya daga cikin 'yan takarar tikitin jam’iyya mai mulki.
A ranar Litinin, Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya ce Lawan ne dan takarar jam’iyyar na maslaha.
Hakan dai ya sabawa yarjejeniyar da gwamnonin jam’iyyar APC suka yi na neman a mika tikitin takarar shugaban kasa zuwa kudu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wasu daga cikin mambobin kwamitin ayyuka na jam’iyyar (NWC) sun hada kai da gwamnonin, inda suka ce zabin Adamu “ra’ayinsa ne” kawai ba APC ba.
Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa:
“Sakataren kwamitin karramawa, Sanata Gumel, mataimaki na musamman ga Lawan, Orji Kalu, bulalan majalisar dattawa, da Hope Uzodimma, suna aiki don ganin cewa deliget da za su kada kuri’a ga Lawan ne kawai za su shiga dandalin Eagle Square."
A baya dai rahoton Leadership ya bayyana cewa, akalla akwai deliget 2,340 da za su kada kuri'a a zaben fidda gwanin na shugaban kasa a APC.
Za ku taro rikici: Yahaya Bello ya fadi abu daya da zai hana shi takara a zaben fidda gwanin APC
A wani labarin, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya gargadi jam'iyyar APC, cewa cire sunansa a jerin 'yan takarar shugaban kasa da za su gwabza a zaben fidda gwani na yau daidai yake yake da kunno wutar rikici, Vanguard ta ruwaito.
Gwamna Bello, wanda yana daya daga cikin ’yan takara 23 a jam’iyyar, ya ce akwai makarkashiyar da ake shirya masa, inda ya zargi gwamnonin APC na Arewa da wasu jiga-jiga da kitsa manakisa akansa.
Bello wanda ya bayyana kansa a matsayin dan takara mafi karbuwa da zai yi nasara idan har tsarin ya tafi daidai, ya ce abu daya ne zai hana shi ya tsaya takarar shugaban kasa shi ne idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya janye daga takarar, inji The Nation.
Asali: Legit.ng