Zaben fidda gwanin APC: 'Yan takara na ta bin deliget har otal domin neman hadin kai

Zaben fidda gwanin APC: 'Yan takara na ta bin deliget har otal domin neman hadin kai

  • Gabannin fara zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, masu neman tikitin jam'iyyar sun fara isa ga deliget a masaukinsu domin kama kafa da su
  • An tattaro cewa yan takarar ta hannun wakilansu sun gabatarwa deliget da na cin abinci kafin a shiga ainahin abun
  • Sai dai kuma, wata majiya ta ce suna isa ga deliget din ne ta hannun gwamnonin jihohinsu da kuma jagororin jam'iyyar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - A yau Talata, 7 ga watan Yuni ne jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ke gudanar da babban taronta domin fidda dan takararta na shugaban kasa na babban zaben 2023 mai zuwa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa manyan yan takara da suka hada da Bola Tinubu, Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi, Kayode Fayemi da Ahmed Lawan sun fara isa ga deliget ta hannun wakilansu inda suka bi su har dakunansu na otal domin neman hadin kansu gabannin fara zaben.

Kara karanta wannan

2023: Kowa ya cije kan bakansa, an gaza yin sulhu da Tinubu da su Osinbajo a takaran APC

An tattaro cewa yayin da gwamnatocin jihohin da APC ke mulki suka samarwa deliget dinsu masauki, yan takara ne suka kamawa wadanda suka fito daga jihohin da ba na APC ba dakuna a otal.

Zaben fidda gwanin APC: 'Yan takara na ta bin deliget har otal domin neman hadin kai
Zaben fidda gwanin APC: 'Yan takara na ta bin deliget har otal domin neman hadin kai Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Wani dan majalisa, wanda ya kasance kodinetan daya daga cikin masu neman takarar, ya bayyana cewa sun baiwa deliget dan kudi da za su ci abinci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Ba mu fara ainahin abun ba amma mun yayyafa ruwa a kasa.”

Wata majiya ta ce an isa ga deliget ne ta hannun gwamnoninsu.

Ya ce:

“Ba kai tsaye muke zuwa ba. Kun san cewa mun hadu da kusan dukkanin deliget din a lokacin rangadinmu na jiha. Don haka, duk abun da za mu yi a yanzu ta hannun gwamnonin ne. sannan a jihohin da bamu da gwamnoni, muna isa gare su ta shugabanninsu na jihohi.”

Kara karanta wannan

Hotuna: 'Yan a mutun Jonathan sun mamaye hedkwatar APC suna neman a ba shi tikiti

Gwamnonin APC sun gabatarwa Buhari jerin sunayen yan takarar shugaban kasa 5

A wani labarin, gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun gabatar da sunayen yan takarar shugaban kasa guda biyar a gaban shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya zabi dan takarar maslaha daga cikinsu, Daily Trust ta rahoto.

Wata majiya abun dogaro ta bayyana cewa gwamnonin sun gabatar da sunayen ne a safiyar Talata, 7 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng