Zabo dan takara: Buhari ya shiga ganawar sirri da gwamnonin APC na Arewa
- Rahotanni daga kafafen sada zumunta sun bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin APC na Arewa
- Wannan na zuwa ne kafin fara zaben fidda gwani, domin dinke wasu matsaloli da suka taso a jam'iyyar APC
- An ruwaito cewa, gwamnonin APC sun dage cewa, dole ne APC ta mika tikitin takara zuwa yankin Kudu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT, Abuja - A halin yanzu dai shugaban kasa Muhammadu Buhari na ganawa da gwamnonin jam'iyyar APC na yankin Arewa a fadar gwamnati dake Abuja.
TheCable ta fahimci cewa taron yana gudana ne a ofishin shugaban kasa.
Ana kyautata zaton manufar taron ya ta'allaka ne kan matakin da gwamnonin Arewa suka dauka na ganin an mika tikitin shugabanci zuwa Kudu.
A ranar Asabar din da ta gabata ne gwamnonin suka bukaci Buhari da ya dubi 'yan takarar shugaban kasa a kudancin kasar a lokacin da yake tunanin zabar magajinsa na zaben 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Su waye gwamnonin da ya shiga ganawa dasu?
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Filato, Simeon Lalong, Abubakar Baduru (Jigawa) da Babagana Zulum (Borno).
Sauran sun hada da Aminu Bello Masari (Katsina), Abdullahi Sule (Nasarawa), Bello Matawale (Zamfara), Malam Nasir el-Rufai (Kaduna) da Abdullahi Ganduje (Kano)
Hakazalika da Yahaya Inuwa (Gombe), Abubakar Bello (Niger), Jihar Yobe. Gwamna, Mai Mala Buni da Abdullrahman Abdulrazak (Kwara).
A lokacin da ake hada rahoton nan, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello bai iso ba, inji rahoton The Guardian.
Shirin 2023: APC ta magantu kan batun takarar Jonathan a zaben fidda gwanin shugaban kasa
A wani labarin, kwamitin tantance 'yan takarar shugaban kasa a APC a ranar Juma’a ya musanta batun tantance tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan cikin 'yan takara.
Shugaban kwamitin tantancewar, John Odigie-Oyegun, ne ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a a lokacin da ya mika rahotonsa ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abduallahi Adamu, a wani taron kwamitin ayyukan jam'iyyar na kasa.
Odigie-Oyegun ya shaidawa manema labarai cewa sabanin labaran da ake yadawa, tsohon shugaban bai halarci taron tantancewan da aka yi Transcorp Hilton ba, inji rahoton Punch.
Asali: Legit.ng