2023: Da yuwuwar a samu maslaha kan wanda zai gaji shugaba Buhari yau, Gwamna Umahi

2023: Da yuwuwar a samu maslaha kan wanda zai gaji shugaba Buhari yau, Gwamna Umahi

  • Gwamna kuma ɗan takarar shugaban kasa, Dave Umahi, ya ce wataƙila zuwa anjima su sanar da ɗan takarar da suka yi sulhu
  • Jam'iyyar APC na cigaɓa shirye-shiryen zaɓen fitar ɗan takarar shugaban ƙasa, amma Buhari ya buƙaci su yi sulhu tsakanin su
  • Gwamnan ya kuma bayyana rashin jin dadinsa bisa cigaba da yaɗa ƙaryar cewa ya janye daga takara

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, ya ce da yuwuwar yau a samu sulhu kan ɗan takarar shugaban ƙasa da zai rike tutar jam'iyyar APC a babban zaɓen 2023.

Umahi, wanda yana ɗaya daga cikin masu hangen tikitin APC, ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a cikin shirin Channels tv ranar Litinin da safe.

Jam'iyyar APC ta tsara gudanar da zaɓen fitar da ɗan takararta na shugaban ƙasa ranar Talata, amma Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bukaci yan takara su yi sulhu.

Kara karanta wannan

Taron APC: Har yanzu Buhari bai zartar da hukunci kan mika mulki kudu ba - Badaru

Gwamna Umahi da Sanata Lawan.
2023: Da yuwuwar a samu maslaha kan wanda zai gaji shugaba Buhari yau, Gwamna Umahi Hoto: Ebonyi online/facebook
Asali: Facebook

Daily trust ta rahoto cewa duk da jerin tarukan da yan takarar suka gudanar domin masalaha tsakanin su, har yanzun bai haifar da ɗa mai ido ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Umahi ya ce:

"Ina ganin nan da awanni 12 zuwa 24, ikon Allah da ɗan takarar maslaha zai bayyana ta hanyar lumana da kuma bin matakan da mafi yawan yan takara idan ba duka ba zasu amince."
"Babu wanda ya fi karfin jam'iyya kuma ya zama wajibi mu yi wa jam'iyya biyayya kuma hakan shi ne gina hanyar sulhu da girmama shugabannin jam'iyya da yan Najeriya."

Ya kara da cewa gwamnonin arewa sun yi iyakar bakin kokarin su na matsawa sai an kai tikitin takara kudancin Najeriya saboda dai-daito da adalci.

Daga nan kuma gwamnan ya yi kira da yan takarar shugaban kasa daga kudu su bar yankin kudu maso gabas ya samu nashi adalcin da daidaito.

Kara karanta wannan

Abin da 'yan takara suka faɗa wa Buhari game da wanda zai zaɓa ya gaje shi a 2023, Yahaya Bello

Ban janye daga takara ba - Umahi

Gwamnan ya kuma nuna rashin jin daɗinsa kan cewa wasu bara gurbi sun sake yaɗa ƙarya game da janyewarsa daga takara a kafafen sada zumunta.

Gwamnan Ebonyi ya jaddada cewa shi ɗan takara ne mai nasara, shiyasa yan adawa da shi ke kokarin yaɗa karyar cewa ya janye daga takara.

"Wannan shi ne karo na uku da wasu ke yaɗa cewa na janye daga takara kuma hakan ya ƙara nuna cewa mutane na shakkar takarata."

A wani labarin kuma Malam Shekarau da sauran yan takara biyu da suka lashe tikitin Sanata a zaɓen fidda gwanin NNPP a Kano

Tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya samu nasara a zaɓen fitar da yan takarar Sanata na jam'iyyar NNPP da wasu mutum biyu.

Shekarau wanda ya fice daga jam'iyyar APC kwanakin baya, ya lashe tikitin ne ba tare da hamayya a Gezawa, Hedkwatar ƙaramar hukumar Gezawa a Kano.

Kara karanta wannan

Ta Fasu: Majiyar Cikin Gida Ta Fallasa Sunan 'Dan Takarar da Buhari ya Karkata Hankali Wurinsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel