Zaben Fidda Gwani: Matasan Kano Sun Balle Zanga-Zanga kan Hukuncin Gwamnonin APC
- Wata kungiyar matasan APC ta jihar Kano ta yi zanga-zangar lumana a Kano inda suke kalubalantar shawarar da gwamnoni 11 na APC da suka yanke na mika mulki ga Kudu
- A cewar shugaban kungiyar, Nura Bebeji, an yanke shawarar ne don kange 'yan takara masu jini a jika irin su Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi daga takarar shugaban kasa
- Nura ya ce wadannan ne gwamonin da suka gaza magance matsalar kashi daya bisa uku na yankin da hatsabibanci ya yi kamari irin su Kano, Zamfara, Sakkwoto, Katsina, Kaduna
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kano - Wata kungiyar da ake wa lakabi da matasan da suka damu da lamurran APC sun shirya zanga-zangar lumana a Kano inda suke kalubalantar shawarar da gwamnoni sha daya na jam'iyya mai mulki ta APC da suka yanke na mika mulki ga kudancin Najeriya, Vanguard ta ruwaito.
Yayin zantawa da manema labarai a wajen zanga-zangar a ranar Lahadi, shugaban kungiyar, Nura Bebeji ya ce yanke shawarar da gwamnonin suka yi sun yi hakan ne da gangan don kange shugabannin arewa masu jini a jika irin su Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi, daga takarar shugabancin kasa.
Ya bayyana cewa duk wani yunkurin da gwamnonin suka yi don hana wa 'yan Najeriya damar zabar ra'ayinsu ba zai haifar da 'da mai ido ba a zaben shekarar 2023 da ke karatowa.
"Mu matasan da suka damu da lamurran APC ne a arewa. Mun fito ne don bayyana rashin jin dadin mu a kan abun da muka ji a kafafan sada zumunta game da shawarar da gwamnoni sha daya suka yanke na mika shugabanci ga kudu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Su ne gwamnonin da ba za su iya lura da lamurran daya-bisa- ukun yankin da 'yan ta'adda, 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke cin karensu ba babbaka ba wadanda suka hada da jihohi irinsu Kano, Zamfara, Sakkwoto, Katsina da sauransu.
"A yanzu ne suke da bakin hada kawuna don mara wa 'dan takarar kudu a APC duk kawai saboda son zuciya.
"Game da wanda za a dauka a matsayin mataimakin shugaban kasa, mu matasan kasa za mu kawai iya amincewa da wanda ya yi muka gani a kasa kuma wanda zai iya magance manyan matsalolin da suka shafi rashin aikin yi, tsaro da hadin kan matasan jam'iyya don shugabanci mai dorewa a 2023.
"Idan jam'iyyar na da ra'ayin kare mutuncin 'yan wasu tsiraru a kan yawancin mutanen jam'iyyar, su tuna da biyayyar da za su sa rai a wuraren zabe" ya tabbatar.
2023: Osinbajo, Tinubu Da Masu Neman Takara Daga Kudu Maso Yamma Za Su Yi Taro Gabanin Zaben Fidda Gwanin APC
A wani labaroi na daban, ana fatan masu neman takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC za su yi taro a yau Asabar. A cewar The Punch, za a yi taron ne misalin karfe 8 na dare a gidan Otunba Osoba, tsohon gwamnan Jihar Ogun.
Wannan cigaban na zuwa ne bayan jam'iyyar na APC ta kammala tantance masu neman takarar shugaban kasar.
A ranar Juma'a, John Oyegun, shugaban kwamitin tantance yan takarar ya sanar da cewa an soke takarar mutum 10 cikin masu neman takarar 23 da ake fatan za su fafata a zaben fidda gwanin.
Asali: Legit.ng