Yanzu: Gwamnonin APC Na Arewa Sun Goyi Bayan Mulki Ya Koma Kudu, Sun Buƙaci Ƴan Takara Daga Arewa Su Janye
- Wasu gwamnonin jihohin arewa a jam'iyyar APC sun bukaci jam'iyyar APC ta mika tikitin takara ga yankin Kudu a 2023, sun kuma yi kira ga yan arewa su janye
- Gwamnonin sun cimma wannan yarjejeniyar ne yayin wani taro da suka yi a karshen mako gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa a APC
- A cewarsu, karamci da adalci ne a mika wa kudun mulki bayan shekaru takwas na shugaba Muhammadu Buhari kuma hakan zai karfafa jam'iyyar APC
Gwamnonin jihohin arewa na jam'iyyar APC sun nuna goyon bayansu ga zaben dan kudu a matsayin wanda zai yi wa jam'iyyar takarar shugaban kasa a 2023.
Gwamnonin sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da suka fitar bayan wani taro da suka yi a ranar Asabar.
Gwamnonin arewa da suka goyi bayan mulki ya koma kudu
2023: El-Rufai, Zulum da sauran gwamnonin arewa masu goyon bayan kudu maciya amana ne – Kungiyar arewa
Takardar na dauke da sa hannun gwamnoni kamar haka: Gwamnan Katsina Bello Aminu Masari; Gwamnan Niger, Abubakar Sani Bello; Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule; Gwamnan Borno, Babagana Zulum; da Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sauran sun hada da Gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya; Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle; Gwamnan Plateau, Simon Lalong; Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje; da Gwamnan Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.
Gwamnonin na Arewa sun bukaci yan takarar shugaban kasa daga arewa sun janye takararsu su bar dan Kudu.
"Bayan kyakyawan nazari, muna son mu bayyana cewa bayan shekaru takwas na Shugaba Muhammadu Buhari, ya kamata a mika wa jihohin kudu damar fitar da dan takarar shugaban kasa.
"Wannan batun karamci ne a APC, matakin da muka dauka ba wai don la'akari da abin da wata jam'iyya ta yi ba.
"Munyi imanin cewa daukan wannan matakin zai karfafa kasa tare da hadin kai da cigaba.
"Don haka muna son mu shawarci Shugaba Muhammadu Buhari ya zabo wanda ya ke son ya gaje shi a matsayin dan takarar shugaban kasa na APC daga jihohin yan uwan mu na kudu.
"Muna kira ga masu neman takara daga jihohin arewa su janye takararsu saboda cigaban kasa, su kyalle yan takara daga kudu su fafata a zaben fidda gwani," wani sashi na jawabin gwamnonin.
Sanarwar ta ce Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammadu Badaru ya janye daga takarar saboda ya bada gudunmawarsa wurin kishin kasa.
Osinbajo Ya Yi Ganawar Sirri Da Shugaban APC Da Gwamnoni 5 a Ofishinsa
A bangare guda, Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a halin yanzu yana ganawa da a akalla gwamnonin jam'iyyar APC guda biyar da Sanata Abdullahi Adamu shugaban jam'iyyar APC na ƙasa a ofishinsa.
Taron na zuwa ne kwanaki biyu bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin a dakin taro na Council Chambers a gidan gwamnati a ranar Talata kafin ya tafi Madrid, Spain.
Hakan kuma na zuwa ne bayan kammala tantance yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC da kwamitin John Odigie-Oyegun ta yi.
Asali: Legit.ng