Babu 'dan takarar da APC ta yi watsi da shi yayin tantancewa, Mamban Kwamitin Tantancewa

Babu 'dan takarar da APC ta yi watsi da shi yayin tantancewa, Mamban Kwamitin Tantancewa

  • Kwamitin tantancewar jam'iyyar APC ba ta hana wani dan takara ba cikin jerin 'yan takara 23 na shugabancin kasa da su ka bayyana gabanta
  • Wani mamban kwamitin ya shaida wa manema labarai cewa, shawartar wasu mutum 13 suka yi su janye daga takarar domin ba za su yi nasara ba
  • A cewarsa, duk jerin 'yan takarar da su ka gabatar da kansu gaban kwamitin su na da cancantar da ya dace su tsaya takarar shugabancin kasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Wani mamban kwamitin tantancewa na jam'iyyar APC ya yi karin haske dangane da batun jam'iyyar na dakatar da wasu 'yan takarar shugaban kasa cikin mutane 23 da suka bayyana gabanta.

Ya bayyana wa Premium Times a daren Juma'a cewa, ba daidai ba ne rahoton da aka dinga yadawa dangane da cewa kwamitin ta dakatar da 'yan takara 13.

Kara karanta wannan

Hotuna: 'Yan a mutun Jonathan sun mamaye hedkwatar APC suna neman a ba shi tikiti

Babu 'dan takarar da APC ta yi watsi da shi yayin tantancewa, Mamban Kwamitin Tantancewa
Babu 'dan takarar da APC ta yi watsi da shi yayin tantancewa, Mamban Kwamitin Tantancewa. Hoto daga Premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mamban wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce duk jerin 'yan takarar shugabancin kasar da suka gabatar da kawunansu gaban kwamitin sun cancanci tsayawa.

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sai dai bisa ganin da kyar su samu nasarar lashe zaban shugaban kasa a jam'iyyarmu, mun gano cewa mutane 13 cikinsu ba za su iya ba, hakan ya sa mu ka shawarce su da su hakura su bar wa wasu.
"Mun yi hakan ne don mu yi tankade da rairaya maimakon jam'iyyar ta dauki mutane 23 a matsayin 'yan takarar zaben fid da gwani, abin zai yi yawa."

Kamar yadda majiyar ta nuna, duk wadanda aka shawarta ba a tilasta musu amfani da shawarar ba.

"Mun gama tantancesu akan cewa duk za su iya takara kuma jam'iyyar za ta ba su shaidar tantancewa. Ba za mu iya dakatar da wani cikin mutane 13 daga yin zaben fidda gwani ba duk da shawarar da mu ka ba su idan sun nuna su na son yi," a cewar majiyar.

Kara karanta wannan

2023: Kwamitin tantancewar APC ya kori 10 daga cikin 'yan takarar shugaban kasa

Mamban ya kara da cewa, shugaban kwamitin tantancewar ya shaida hakan ranar Juma'a yayin gabatar da rahoton kwamitin ga shugaban jam'iyyar na kasa, Abdullahi Adamu, amma sai manema labarai su ka sauya maganar.

Ya ci gaba da cewa, shugabancin jam'iyyar ya nemi a shawarci akalla mutane 10 su janye saboda da kyar ko sun tsaya su lashe zaben.

Ni a suwa: Ba zan taba kuskura na raina shugaba Buhari ba, inji Bola Tinubu

A wan labari na daban, Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas da ke neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya ce ba zai yiwu ba ya raina shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya, TheCable ta ruwaito.

Tinubu ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, dangane da kalaman sa da ya yi a taron da ya yi da deliget-deliget na jam’iyyar APC a jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen 'yan takara 5 da ake sa ran Buhari zai zabi daya don ya gaje shi

A ganawar da ya yi da su a ranar Alhamis, Tinubu ya ce in ba dan shi ba, da Buhari ya fadi zaben shugaban kasa a 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng