2023: INEC ta saki jerin ka'idojin zabuka, ta sanar da irin takardun kuri'u da za a kirga

2023: INEC ta saki jerin ka'idojin zabuka, ta sanar da irin takardun kuri'u da za a kirga

  • Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta saki yardaddun ka'idojin da zasu taimaka wurin aiwatar da zaben 2023 mai matsowa lafiya
  • Kamar yadda ka'idojin su ka nuna, wajibi ne shugaban akwatin zabe, PO ya kirga yawan takardun zabe wadanda ke dauke da hatimin hukumar
  • Sannan kuma ba a yarda da amfani da wayar salula ba a harabar zabe ko kuma wata na'urar da za a iya amfani da ita wurin daukar hotuna

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta fitar da jerin ka'idojin da za a yi amfani da su wurin aiwatar da zaben 2023 na kasa da ke karatowa.

Kamar yadda ka'idojin su ka zo, wajibi ne shugaban akwatin zabe, PO, ya kirga yawan takardun zabe wadanda suke dauke da hatimin hukumar, jaridar Leadership ta ruwaito..

Kara karanta wannan

2023: Kwamitin tantancewar APC ya kori 10 daga cikin 'yan takarar shugaban kasa

A batun amfani da wayoyi yayin zabe, kamar yadda dokokin su ka nuna, wajibi ne kawar da duk wata waya ko na'urar da za a iya amfani da ita wurin daukar hotuna a harabar zabe.

2023: INEC ta saki jerin ka'idojin zabuka, ta sanar da irin takardun kuri'u da za a kirga
2023: INEC ta saki jerin ka'idojin zabuka, ta sanar da irin takardun kuri'u da za a kirga. Hoto daga leadership.com
Asali: UGC

Sannan dokar ta tabbatar da cewa ba za ayi amfani da sakamakon wani akwati ba wanda yawan kuri'u ya zarce yawan masu zaben da aka tantance, kuma wajibi ne jami'in da ke da alhakin tattara kuri'u ya bayar da rahoto idan hakan ya auku.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka zalika tazarar da ke tsakanin 'yan takara biyu wadanda su ka fi yawan kuri'u kamar yadda dokar ta tanadar, ba yawan masu zaben da su ka amshi katinan zabensu ba ne (PVCs) a wurin zaben da aka dage zabe, ko aka rushe shi ko kuma ba a gudanar da shi ba kamar yadda sashi na 24(2 & 3), 47(3) da 51(2) na dokar zaben 2022 ya tanadar.

Kara karanta wannan

Zamfara: Dumu-dumu an kama magidanci da sassan jikin mutum

Wajibi ne baturen zabe ya dakata har sai an gudanar da zabe a akwatinan kuma an tattaro sakamakon a cikin fom din da ya dace sannan a gabatar da shi.

A cewarsa:

"Wannan shi ne tazarar da ke tsakanin 'yan takara biyu mafi yawan kuri'u kuma haka za a yi a ko wanne zabe, a ci gaba da bin wadannan dokokin da ka'idojin."

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya gabatar da wadannan jerin dokokin ne a Abuja yayin wani taro na musamman da aka yi da Kwamitin tuntubar kungiyoyi akan tsaron zabe (ICCES) don tabbatar da tsaron zaben gwamnonin da za a yi a jihar Ekiti.

Channels TV ta rahoto cewa, Yakubu ya ce gabatar da ka'idojin na nuna cewa hukumar ta kammala duk wasu shirye-shiryen aiwatar da zabe a akwatina.

Yayin da ake kokarin kafa dokar zaben 2022, ya ce wajibi ne hukumar ta sake duba dokokin zaben da za su taimaka wurin aiwatar da zabe mai zuwa lafiya.

Kara karanta wannan

Yadda Atiku ya yi amfani da dabara daf da mintin karshe, ya doke Wike a zaben fitar da gwani

A cewarsa, da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka gyara), dokokin zabe na 2022 da kuma ka'idojin aiwatar da zaben su ne hanyoyin da za a yi amfanu da su wurin shirya babban zabe mai karatowa.

Ni a suwa: Ba zan taba kuskura na raina shugaba Buhari ba, inji Bola Tinubu

A wani labari na daban, Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas da ke neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya ce ba zai yiwu ba ya raina shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya, TheCable ta ruwaito.

Tinubu ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, dangane da kalaman sa da ya yi a taron da ya yi da deliget-deliget na jam’iyyar APC a jihar Ogun.

A ganawar da ya yi da su a ranar Alhamis, Tinubu ya ce in ba dan shi ba, da Buhari ya fadi zaben shugaban kasa a 2015.

Kara karanta wannan

Da duminsa: EFCC ta yi ram da tsohon gwamna kan zargin hannu a damfarar N80b ta dakataccen AGF

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng