Ni a suwa: Ba zan taba kuskura na raina shugaba Buhari ba, inji Bola Tinubu

Ni a suwa: Ba zan taba kuskura na raina shugaba Buhari ba, inji Bola Tinubu

Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas da ke neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya ce ba zai yiwu ba ya raina shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya, TheCable ta ruwaito.

Tinubu ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, dangane da kalaman sa da ya yi a taron da ya yi da deliget-deliget na jam’iyyar APC a jihar Ogun.

A ganawar da ya yi da su a ranar Alhamis, Tinubu ya ce in ba dan shi ba, da Buhari ya fadi zaben shugaban kasa a 2015.

Shugaba Buhari ba abin rainawa bane
Ni a suwa: Ba zan taba kuskura na raina shugaba Buhari ba, inji Bola Tinubu | Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Sai dai a cikin sanarwar da ke fayyace kalaman nasa, Tinubu ya ce ba wai yana nufin muzanta shugaban kasa Buhari bane.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Ba Zan Taɓa Raina Buhari Ba, In Ji Bola Tinubu

A cewarsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Ina alfahari da matsayi na wajen kawo jam’iyyar APC da kuma nasarorin da ta samu a zabe. Amma ba shakka shugaba Buhari ya tsaya a matsayin babban ginshikin wannan nasara.
“An zabe shi shugaban kasa har sau biyu. Ya dauki nauyin mulkin kasa tsawon shekaru bakwai. Babu wani abu da zai iya hamayya da hakan. Ba zan kuskura in raina abin da ya yi da abin da yake nufi ga jam’iyya da kasa ba.”

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.