Saura kwana biyu zaben fidda gwanin APC: Adadin deleget da kowace jiha ke da shi

Saura kwana biyu zaben fidda gwanin APC: Adadin deleget da kowace jiha ke da shi

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi watsi da tsarin kato bayan kato wajen zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na zaben 2023 sabanin yadda tayi a zaben 2019.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jam'iyyar ta yanke shawarar amfani da deleget wajen zaben wanda zai wakilci jam'iyyar a zaben shugaban kasa.

An yanke shawarar haka ne a taron Majalisar zartaswa NEC ta 11 da ya gudana a Transcorp Hotel a watan Afrilu a birnin tarayya Abuja.

Kundin tsarin mulkin jam'iyyar APC ya bada zabi uku na yadda za'a gudanar da zaben fidda gwani.

Ittifaki, yar tinke wanda aka fi sani da kato bayan kato, da kuma na deleget.

Jam'iyyar APC na da Deleget 7,800.

Yayinda jihar Kano tafi yawan deleget, Abuja ke da mafi karanci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Bayan canza zaɓe, Ɗan tsohon gwamna ya lallasa tsohon shugaban FCC, ya lashe tikitin takarar gwamna a 2023

Saura kwana biyu zaben fidda gwanin APC: adadin deleget da kowace jiha ke da shi
Saura kwana biyu zaben fidda gwanin APC: adadin deleget da kowace jiha ke da shi Hoto: Professor Yemi Osinbajo
Asali: Twitter

Legit ta tattaro muku adadin deleget da kowace jiha ke da shi:

Kano: 465

Katsina: 384

Borno: 324

Osun: 308

Lagos: 304

Oyo: 292

Jigawa: 266

Niger: 251

Ogun: 248

Nasarawa: 245

Abia: 154

Adamawa: 184

Akwa Ibom: 165

Anambra: 163

Bauchi: 202

Bayelsa: 79

BenueL: 180

Cross River: 194

Delta: 170

Ebonyi: 154

Edo: 168

Ekiti: 216

Enugu: 131

Gombe: 134

Imo: 236

Kaduna: 234

Kebbi 213

Kogi: 222

Kwara: 195

Ondo: 200

Plateau: 185

Rivers: 151

Sokoto: 193

Taraba: 146

Yobe: 222

Zamfara: 169

FCT: 53

Shugaba Buhari ya faɗa mana ɗan takarar da yake so ya gaje shi, Gwamna Sule

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya faɗa wa gwamnonin APC ɗan takarar da yake so yayin da jam'iyya ke fuskantar zaɓen fid da gwani.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar SDP Ta Tsayar Da Gogaggen Sanata Takarar Shugaban Kasa

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a wurin hira da kafar watsa labarai ta Talabijin wato Channels tv cikin shirin su na 'Siyasa a yau' ranar Talata.

Shugaban ƙasa Buhari ya gana da gwamnoni 22 na jam'iyyar APC ranar Talata domin tattaunawa kan zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban kasa da kuma bukatar su cimma matsaya guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng