2023: Fitaccen dan siyasar arewa ya lissafa yan takarar APC 4 da za su iya tikar da Atiku a kasa
- Tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, Farouk Aliyu, ya nuna karfin gwiwar cewa APC za ta ci gaba da shugabancin kasar a 2023
- Aliyu ya ce jam’iyyar na da akalla yan takarar shugaban kasa biyar da za su iya kayar da Atiku idan har suka mallaki tikiti a 2023
- Sai dai kuma, ya yarda cewa ba za a iya raina karfin dan takarar na PDP kuma tsohon shugaban kasar ba
Farouk Aliyu, tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, ya ce jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki na da yan takara biyar da za su iya lallasa dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, a 2023.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ne ya mallaki tikitin PDP na babban zaben 2023 mai zuwa bayan ya kasar da babban abokin hamayyarsa kuma gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike.
Shugabanci a 2023: Obasanjo na bakin ciki da yadda Atiku ya samu tikitin takara a PDP, yana shirya masa tuggu
A wata hira da Channels TV, Aliyu ya lissafa yan takara hudu cikin biyar da yake ganin za su iya kayar da Atiku idan suka lashe tikitin jam’iyyar mai mulki.
Yan takarar sune:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
- Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo
- Asiwaju Bola Tinubu
- Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi
- Tsohon karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba
Ya ce:
“Muna da mutane fiye da guda biyar a APC da za su iya kayar da Atiku Abubakar, Amaechi, Bola Tinubu, Emeka Nwajiuba, mataimakin shugaban kasa Osinbajo za su iya.”
Asali: Legit.ng