Zaben fidda gwanin APC a Kano: An nemi a soke shirin yayin da aka kaddamar da bincike kan kisan mutane 3
- Hukumar kare hakkin dan adam ta kasa da kungiyar KCSF sun kaddamar da bincike kan batun kisan mutane uku a yayin zaben fidda gwanin jam'iyyar APC a jihar
- Kungiyoyin sun bayyana cewa ba za su nade hannu suna kallo ba har jihar Kano ta kece da rikicin siyasa ba gabannin 2023
- An kafa kwamitin mutane 11 domin gudanar da binciken gaggawa tare da gabatar da rahotonsu cikin makonni uku
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kano - Hukumar kare hakkin dan adam ta kasa (NHRC), tare da hadin gwiwar kungiyar KCSF, sun kaddamar da wani kwamitin domin bincike cikin lamarin kisan mutane uku yayin zaben fidda dan takarar gwamnan jam’iyyar Progressives Congress (APC) a jihar Kano.
Daily Trust ta rahoto cewa wani dan takarar gwamnna a jam’iyyar, Sha’aban Sharada, ya yi zargin cewa an kashe magoya bayansa yayin da aka jikkata wasu a yayin zaben wanda ya gudana a ranar Alhamis da ta gabata.
The Guardian ta rahoto cewa Shugaban hukumar NHRC, Shehu Abdullahi, ya ce hankalin hukumar bai kwanta da abun da ya biyo bayan zaben fidda gwanin ba wanda ya kai ga salwantar da rayuka.
Shehu ya bayyana cewa NHRC da KCSF sun samu jerin korafe-korafe daga jama’a kan zargin kisan mutane uku da aka yi a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, ya kara da cewa ba zasu zura idanu suna kallo jihar Kano ta kece da rikicin siyasa ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An kafa kwamitin mutum 11 karkashin jagorancin shugaban na NHRC, Shehu Abdullahi, da shugaban KCSF, Ibrahim Waiya.
Waiya ya bayyana cewa ana sanya ran kwamitin zai gabatar da rahotonsa cikin makonni uku don gudanar da binciken lamarin cikin gaggawa.
A halin da ake ciki, wasu kungiyoyi a jihar sun yi kira ga soke zaben fidda gwanin APC a jihar kan zargin aikata magudi a zaben.
Gwamnan Borno a 2023: Dan takarar PDP ya zargi Zulum da son kai, ya sha alwashin tsige sa daga mulki
Kungiyoyin sun yi zargin cewa jami’an gwamnati sun ci zarafin mutane da kuma hana deleget din Sharada kada kuri’a a zaben.
Idan za a tuna, mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna ne ya lashe zaben fidda gwanin.
Bidiyo: Yadda aka tafka magudi, aka yi waje da Hadimin Buhari Bashir Ahmad a zaben fidda gwani a Kano
A gefe guda, tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, a ranar Lahadi ya wallafa bidiyon dake nuna yadda aka yi murdiyar zaben fidda gwanin jam'iyyar APC a mazabar Gaya/Ajingi/ Albasu.
Ahmad, wanda ya yi takarar fidda gwanin ya samu kuri'u 16 yayin da abokin hamayayyarsa Abdullahi Gaya ya tashi da kuri'u 109, a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin.
A cewar Ahmad, ya bar filin zaben tare da magoya bayansa, wadanda a cewarsa 'yan sara-suka sun ci zarafinsu, hakan yasa ya kai kukansa ga shugabannin jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng