Bidiyo: Yadda aka tafka magudi, aka yi waje da Hadimin Buhari Bashir Ahmad a zaben fidda gwani a Kano

Bidiyo: Yadda aka tafka magudi, aka yi waje da Hadimin Buhari Bashir Ahmad a zaben fidda gwani a Kano

  • Tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya koka a kan yadda aka tafka magudi a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC na mazabar Gaya/Ajingi/Albasu
  • Ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook inda ya wallafa bidiyon da ke nuna yadda wani wakilin zabe ke ta kada kuri'u a kan layin zaben shi kadai
  • Ya yi korafin a kan yadda aka ci zarafin deliget mabiyansa a filin zaben, hakan yasa suka bar wurin ba tare da an kammala ba, ya tashi da kuri'u 16

Tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, a ranar Lahadi ya wallafa bidiyon dake nuna yadda aka yi murdiyar zaben fidda gwanin jam'iyyar APC a mazabar Gaya/Ajingi/ Albasu.

Ahmad, wanda ya yi takarar fidda gwanin ya samu kuri'u 16 yayin da abokin hamayayyarsa Abdullahi Gaya ya tashi da kuri'u 109, a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin.

Kara karanta wannan

Shugabancin kasa a 2023: Wike da wasu 'yan siyasa 4 da ka iya zama abokan takarar Atiku

Bidiyo: Yadda aka tafka magudi, aka yi waje da Hadimin Buhari Bashir Ahmad a zaben fidda gwani a Kano
Bidiyo: Yadda aka tafka magudi, aka yi waje da Hadimin Buhari Bashir Ahmad a zaben fidda gwani a Kano. Hoto dga @BashirAhmaad
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Ahmad, ya bar filin zaben tare da magoya bayansa, wadanda a cewarsa 'yan sara-suka sun ci zarafinsu, hakan yasa ya kai kukansa ga shugabannin jam'iyyar APC.

Ya bukaci a sake zaben

Ya ce ya bi duk hanyoyin da zai iya wadanda suka dace don ganin an kwatar masa hakkinsa da yake zargin wadanda suka yi nasarar sun danne.

"A matsayina na 'dan takara, na bar filin zaben fidda gwanin mazabar Gaya, Ajingi da Albasu saboda tsare lafiyar yawancin wakilan zabe na, idan kana so ka yi gogayya yadda ya dace, ba sai ka saka 'yan sara suka a cikin wani zabe ba," Ahmad ya rubata hakan a shafinsa na Facebook.

Bidiyon ya nuna yadda wani mutumi ya bayyana yana mai jujjuwa kuri'u ta hanyar zaben mutane da dama, wanda ake tunanin wakilin zabe ne a kan layin kada kuri'u.

Kara karanta wannan

Gwamnan Plateau: Masu neman tikitin APC 18 sun yi watsi da zaben fidda gwanin jam’iyyar

Ta bayan fagen bidiyon, an ji wata murya na cewa wannan shi ne zaben fidda gwani na Gaya/Ajingi/Albasu.

Sai dai, wannan jaridar ba zata iya gano wakilin waye daga cikin 'yan takarar ya ke zabe fiye da ka'ida ba.

Zaɓen Fidda Gwanin APC: Da Ƙyar Na Sha, Dole Na Tsere Don Kada a Kashe Ni, In Ji Ɗan Majalisa

A wani labari na daban, Mayiwa Lawson Alade, dan majalisa mai wakiltar Akure ta Kudu da kuma Akure da Arewa a Jihar Ondo, kuma dan takarar APC a zaben fidda gwani, ya labarta yadda ya sha da kyar yayin da aka yi yinkurin halaka shi ana tsaka da zaben fidda gwanin jam’iyyar.

Hakan ya sa Lawson ya nemi jam’iyyar ta rushe zaben kuma ta wofantar da shi kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Ya sanar da manema labarai da tsakar daren jiya cewa ana tsaka da zaben, ‘yan bangar siyasa su ka kai farmaki bayan sun ga ya na gab da cin nasara.

Kara karanta wannan

2023: Dattijo ya lashe tikitin APC na sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel