2023: Shugaban majalisa ya tura wa deliget wasika kan zaben fidda gwanin APC
- Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya tura wasika ga deliget na jam'iyyar APC kan shugaban da za su zaba
- Ya bayyana cewa, ya kamata su dage su ajiye batun kudi a gefe su zabi shugaban da zai shugabanci Najeriya ba mulkar 'yan kasa ba
- Ya kuma bayyana bukatar deliget-deliget din da su duba shugaban da ba dauke da wani kaya a kansa na rashawa da almundahana
Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya aika wasika mai zafi ga deliget-deliget na jam’iyyar APC da su yi la’akari da tarihin ‘yan takara da kuma bayanai kafin kada kuri’a a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar da ke tafe.
A wata wasika a ranar Laraba, dan takarar shugaban kasar ya nemi kuri’un deliget-deliget domin ya samu damar zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2023, Punch ta ruwaito.
Ya kuma bukace su da su zabi mutumin da zai yi shugabanci ba mulkin ’yan Najeriya ba da kuma “shugaban da ba shi da kaya kwata-kwata a kansa”.
Sanarwar da jaridar Vanguard ta yada ta kara da cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ga daukacin deliget-deliget a fadin Najeriya, ina rokon ku da ku ajiye batun cika aljihu da kudi a gefe kuma ku yi la’akari da abin da ‘ya fi dacewa wajen neman shugaba ba dan siyasa ba.
“Ina rokonka da ka zabi mutumin da zai yi shugabanci ba mulkin ‘yan Najeriya ba; wanda zai kasance mai fahimta, juriya, adalci, gaskiya, da ci tunanin gaba. Shugaban da ya zo da cikakken da 'bai dauke da kaya.'"
Dan takarar APC: Abu mai sauki ne na lallasa Atiku a zaben 2023, a bani tikiti kawai
A wani labarin, wani rahoton Punch ya ce, Fasto Tunde Bakare, ya bayyana kwarin gwiwar ganin ya kayar da dan takarar shugaban kasa na PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, idan har aka ba shi tikitin jam’iyyar APC.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai, dan takarar shugaban kasar ya bayyana gamsuwa da tsarin tantancewar da APC ta gudanar.
Ya bayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya cancanta a amtsayin abokin gwabzawa.
Asali: Legit.ng