Jigon APC: Kada ku mai da zaben fidda gwanin shugaban kasa dandalin ruwan daloli
- Wani jigon APC ya bayyana bukatar hadin kai tsakanin jam'iyyar da kuma kishin kasa a kan gaba da komai
- Ya bayyana cewa, ya kamata APC ta sanya ido kada zaben fidda gwnainta ya zama irin na jam'iyyar PDP da aka kammala
- Ya kuma ce, kada jam'iyyar ta bari filin zaben fidda gwanin ya zama dandalin ruwan daloli kamar na PDP
Abuja - Daily Sun ta rahoto cewa, jigon jam’iyyar APC, Mista Gbenga Olawepo-Hashim, ya yi gargadin cewa kada zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ya zama wani taron ruwan daloli da kuma dandalin ciniki.
A wata sanarwa da ta fito daga ofishinsa da ke Abuja, a ranar Talata, ya bayyana cewa, kasar nan ba wata kaya ce da za a yi cinikinta ba, kuma ba wata kadara ce da za a yi gwanjonta ba da sayar da ita ga mai kudi.
Na Yi Matuƙar Takaicin Yadda Daliget Ɗin Jihar Mu Ba Su Zaɓe Ni Ba, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na PDP
Ya kuma kara da cewa, ba a taba sayar da shugabancin kasa ba ba za a fara ba yanzu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
A cewarsa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Jam’iyyar PDP ta nuna cewa ba ta koyi komai ba, amma, a matsayinta na jam’iyya, APC ba za ta yi koyi da wannan abin kunya ba. Dole ne shugaban Najeriya mai jiran gado ya zama ba shugaban kakaba ba. Kada shugaban mu ya zama dan daba!"
Yayin da ya ke bayyana cewa, jam’iyyar APC, kasancewar ta mai shugaban kasa mai ci, ya ce ana sa ran abubuwa da yawa daga gare ta ta fuskar alkibla da shugabanci nagari.
Ya kara da cewa har yanzu gwamnati na da aiki mai yawa da hanyoyin aiwatar da siyasa fiye da dukufa kan tagayyarar da kudi.
Ya kuma bayyana cewa, kamata ya yi jiga-jigai da shugabannin jam'iyyar ta APC su sanya kishin kasa da abinda kasa ke bukata fiye da son ran wani dan takara.
Shirin 2023: Buhari ya shiga ganawa da gwamnonin APC kan zaben magajinsa
A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari a yanzu haka yana ganawa da gwamnonin da aka zaba a karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki.
An tattaro cewa, taron ana yin sa ne kan batun zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar da za a yi a ranakun Talata da Laraba a mako mai zuwa.
Dukkan gwamnonin jam’iyyar APC sun halarci taron kamar yadda jaridar Leadership ta tattaro.
Asali: Legit.ng