2023: Buhari ya lissafa sharuddan da dole 'dan takarar shugabancin kasa na APC ya cika
- Buhari ya ce dole zabin 'dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC ya zama wanda zai sa talakawan Najeriya su ji alamun nasara da natsuwar rai su ko kafin lokacin zabe ya yi
- Ya sanar da hakan yayin ganawa da gwamnonin jam'iyyar 22 inda gwamna Bagudu kuma shugaban kungiyar gwamnoni ya sha alwashin za a yi duk abinda ya dace
- Masu son tsayawa takarar shugaban kasa a APC 23 ne, kuma an fara tantancesu a Abuja, babu tabbacin Okorocha zai samu damar zuwa duba da yadda yake hannun EFCC
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ja kunnen gwamnonin jam'iyyar APC da su tabbatar a zaben fidda gwanin jam'iyyar dake karatowa sun zabi 'dan takarar shugaban kasa wanda ya cancanta kuma ya dace.
Ya kara da cewa, 'dan takarar da ya kamata a zaba shi ne "wanda zai ba talakawan Najeriya natsuwa da jin alamun nasara ko kafin lokacin zabe."
Babban Dan Takarar Shugaban Kasa na PDP Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Ya Sha Kaye a Zaɓen Fidda Gwani na 2023
Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, a wata takarda da ya fita ranar Talata, ya bayyana yadda shugaban kasar ya yi gargadin a ganawar da ya yi da gwamnonin jam'iyyar APC da shugaban jam'iyyar na kasa, Abdullahi Adamu, a gidan gwamnati dake Abuja.
Duba da yadda APC za ta yi zaben fidda 'dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar a Abuja tsakanin 6 zuwa 8 ga watan Yuni, yasa Buhari ya bukaci gwamnonin su tabbatar sun hada kawunansu don samun nasarar da tafi wacce aka samu a baya a zaben 2023.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"An jima da fara shirye-shiryen gangamin zaben shekarar 2023, kuma na lura da cewa jam'iyyun da suka fi nasara sun dogara da hadin kan cikin gida tare da shugabanci mai karfi don samun nasarar da tafi ta da a zabe mai karatowa.
"Jam'iyyarmu, APC ba za a barta a baya ba, saboda har yanzu muna cigaba da ganin kasarmu tafi haka.
"A lokacin da na dawo madafun iko a matsayina na shugaban kasar Najeriya sanan shugaban wannan jam'iyyar, na gane yadda ake bukata na da in samar da shugabanci mai karfi ga jam'iyyar karkashin wannan mulki tare da tabbatar da hakan ya faru cikin tsari.
"Wannan shugabanci na bukatar jam'iyyar ta cigaba da karfafa tare da hadin kai.
"Nan da kwanaki kalilan, jam'iyyar zata yi zaben fidda 'dan takarar shugaban kasa wanda zai gabata don zabar wanda zai rike tutar takarar shugaban kasa a gangamin zaben shekarar 2023.
"Wannan abu ne mai mahimmanci, sannan ya kamata sakamakon ya tabbatar wa duniya irin nagartar APC a tsarin siyasa, al'ada bugu da kari shugabanci," a cewar Buhari.
"Dole manufarmu ta zama samun nasarar jam'iyyarmu kuma dole 'dan takararmu ya zama wanda zai ba wa talakawan Najeriya natsuwa da jin alamun nasara ko kafin a zabe shi."
Gwamnan jihar Kebbi kuma shugaban kungiyar gwamnoni, ya ari bakinsu ya ci musu albasa, inda ya ce dole jam'iyyar ta dora daga kan nasarorin da ta samu a zaben fidda gwanin da tayi kwanan nan.
A cewarsa dole jam'iyyar ta tsaida 'dan takarar da zai nuna kauna da kishin kasar kamar yadda shugaban kasar ya nuna.
"Zan marawa shugaban kasa baya don ganin an yi zaben fidda gwanin cikin nasara," ya dauki alkawari.
Duk da 'yan takara 23 ne ke fafutukar ganin sun samu tiketin jam'iyya mai mulkin a halin yanzu.
'Yan takarar sun hada da: Tsohon ministan ilimi na kasa, Chukwuemaka Nwajuiba, Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, Felix Nicholas, fasto dake zaune a Amurka, Tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun;
Gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa, sanata mai ci, Ajayi Borroffice da Tsohon shugaban majalisar dattawa Ken Nnamani.
Saura sun hada da; Uju Ken-Ohaneye, Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi; Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sani Yerima, Tsohon gwamnan jihar Legas, Bol Tinubu da fitaccen faston nan, Tunde Bakare.
Asali: Legit.ng