Shirin 2023: Abin da Buhari ya fada wa gwamnonin APC kan zaben magajinsa
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tofa albarkacin bakinsa kan hanyar da za a bi wajen zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben fidda gwani da za a yi.
Da yake magana da gwamnonin jam’iyyar APC a Abuja a ranar Talata, 31 ga watan Mayu, shugaban ya shawarce su da su mayar da hankali kan sauye-sauyen al’amuran kasar nan da kuma tsammanin ‘yan Najeriya wajen zaben dan takarar.
Ya bukace su da su saka nasara a matsayin babban abin da suka fi mayar da hankali a kai a duk wani fafutukarsu, ya kara da cewa mai rike da tuta dole ne ya zama wanda zai ba da kwarin gwiwa ga mabiya bayansa.
Shugaba Buhari ya ce:
“A cikin ‘yan kwanaki kadan, jam’iyyar za ta gudanar da babban taronta inda za a gudanar da zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa a babban zaben 2023. Wannan tsari ne mai matukar muhimmanci kuma sakamakonsa ya kamata ya tabbatar wa duniya, kyakkyawan ingancin jam'iyyar APC dangane da ka'idojin dimokuradiyya, al'adu da jagoranci."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Karanta cikakkiyar sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar:
Asali: Legit.ng