2023: Duk da nukun-nukun da ake yi, akwai yiwuwar APC ta tantance Jonathan a yau

2023: Duk da nukun-nukun da ake yi, akwai yiwuwar APC ta tantance Jonathan a yau

  • Ba abin mamaki ba ne a ga Dr. Goodluck Ebele Jonathan wajen tantance masu neman takara a APC
  • Goodluck Jonathan ya na kasar waje, amma akwai jita-jitar cewa zai zauna gaban kwamitin an jima
  • Har yau an rasa gane gaskiyar lamari a kan neman takarar tsohon shugaban kasa a zaben 2023

Abuja - Akwai alamu da ke nuna babu mamaki Goodluck Jonathan ya bayyana a gaban kwamitin APC na tantance masu neman kujerar shugaban kasa.

Leadership a rahoton da ta fitar a safiyar Talata, 31 ga watan Mayu 2022, ta ce akwai yiwuwar Goodluck Jonathan yana cikin wadanda za a tantance.

A ranar Litinin ne aka fara tantance wadanda suke burin yin takara a APC. Kwamitin da suke yi wannan aiki sun tare ne a wani babban otel a Abuja.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Nakiya ta sake tashi a gidan giya yayinda yan PDP ke murnar nasarar Atiku

Rahoton yiwuwar shiga takarar na zuwa ne bayan an ji fadar shugaban kasa ta na nesanta Muhammadu Buhari daga shirin ba Jonathan tikiti.

Jonathan yana Italiya

A halin yanzu tsohon shugaban na Najeriya yana halartar wani taron ECAM da kasashen Turai su ka shirya a kan sha’anin Afrika ta kuma gabas da tsakiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A yau ake sa ran Jonathan zai dawo daga wannan taro da ke gudana a birnin Milan, kasar Italiya.

Goodluck Ebele Jonathan
Goodluck Ebele Jonathan Hoto: www.bloomberg.com

Da zarar ya iso Najeriya, akwai kishin-kishin din zai zarce ne wajen inda kwamitin John Oyegun yake tantance wadanda za su nemi takarar shugaban kasa.

Wata majiya ta shaidawa jaridar wannan, ta ce ba gaskiya ba ne a ce Jonathan bai cikin masu takara, kuma har yanzu ba a cire rai da neman mulkinsa ba.

Wanda ya shaidawa manema labarai wannan bai bari an kama sunansa ba, amma ya tabbatar da cewa Muhammadu Buhari yana goyon bayan takarar Jonathan.

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Shehu Sani ya shawarci Atiku kan irin wanda ya kamata ya zaba a matsayin mataimaki

“A yau yake dawowa, kuma ina tabbatar maku da idan ba abubuwa sun sake zani ba, zai zarce ne wajen tantance masu takarar shugaban kasa a APC.”

- Majiyar

An dauki wata da watanni ana rade-radi kan makomar Goodluck Jonathan a siyasa. Har yanzu tsohon shugaban na Najeriya bai fito da matsaya karara a fili ba.

Jonathan ba 'Dan APC ba ne

A baya an ji labari mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Arewa ta yamma, Salihu Lukman ya ce idan yana nan, Goodluck Jonathan ba zai ji kanshin takara ba.

Salihu Lukman ya ce tsohon Shugaban kasa Jonathan bai cikin ‘ya ‘yan APC da jam’iyyar ta sani, ya ce surutan banza masu maganar takarar ta sa a 2023 suke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng