Shehu Sani ga Atiku: Ka gwangwaje ka zabi abokin gami mai nagarta

Shehu Sani ga Atiku: Ka gwangwaje ka zabi abokin gami mai nagarta

  • Bayan lashe zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, an shawarci Atiku Abubakar da ya zabi abokin takarar da za su hada kai su yi aiki
  • Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta kasa, Shehu Sani, ya bayar da wannan shawarar ne a ranar Litinin, 30 ga watan Mayu
  • Jigon na PDP ya kuma bukaci ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su zabi Atiku su sanya shi ya gaji shugaba Buhari a zaben 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Sanata Shehu Sani, tsohon dan majalisar dattawa daga Kaduna ta tsakiya kuma tsohon dan takarar gwamna, ya shawarci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kan zabin abokin takararsa bayan ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2023 zai iya zama Gwamnan da ya yi takara da shi

Atiku a zaben fidda gwani da aka gudanar a filin wasa na MKO Abiola da ke Abuja a ranar Asabar, 28 ga watan Mayu, ya doke tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da sauran ‘yan takara.

Shehu Sani ya shawarci Atiku
Shehu Sani ga Atiku: Ka gwangwaje ka zabi abokin gami mai nagarta | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Da yake magana a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, 30 ga watan Mayu, Sanata Sani ya shawarci tsohon mataimakin shugaban kasar da ya zabi abokin takarar da zai iya hada kai tare da shi su yi aiki.

Sani wanda ya sha kaye a yunkurinsa na lashe tikitin takarar gwamnan jam'iyyar PDP a jihar Kaduna ya bukaci 'yan Najeriya masu son ganin sabuwar kasa dunkulalliya, mai da zaman lafiya da su zabi Atiku a zaben shugaban kasa na 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya rubuta a Twitter cewa:

"An gama zaben fidda gwani na jam'iyyar adawa. Duk 'yan takara, 'yan jam'iyya da 'yan Najeriya masu son...(Na so in rubuta Canji amma na canza ra'ayi) sabuwar Najeriya mai hadin kai, zaman lafiya da wadata ya kamata ya zabi dan takara Atiku Abubakar. Ga AA kuma, ka zabi VP za ku hada kai ku iya aiki."

Kara karanta wannan

Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

Tinubu: Babu wani cin girma da zan yi, burina kawai na yi takara a zaben 2023 mai zuwa

A wani labarin, rahotanni sun bayyana cewa Bola Tinubu ya dage kan cewa ba zai janye daga takara ba duk kuwa abin da zai faru.

An ce dan takarar na kan gaba a jam’iyyar APC mai mulki ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin tantance 'yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Jaridar Leadership ta yi ikirarin cewa Tinubu ya bayyanawa kwamitin cewa ba zai amince da wata matsaya da za a zo da ita kan 'yan takara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.