Shugabancin kasa a 2023: Wike da wasu 'yan siyasa 4 da ka iya zama abokan takarar Atiku
A ranar Asabar, 28 ga watan Mayu, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya zama zakaran gwajin dafi a zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP na 'yan takarar shugaban kasar shekarar 2023.
Atiku ya samu kuri'u 371, hakan yasa ya lashe zaben 'yan takarar shugaban kasar jam'iyyar PDP da ya gabata a MKO Stadium dake Abuja.
Baya ga nasarar lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP da ya yi, Atiku Abubakar yana fuskantar babban kalubale wajen daukar wanda ya ke so su yi tafiyar tare a matsayin mataimaki.
Bayan nasarar da ya samu, wani babban aiki da ke gaban Atiku shi ne daukar mataimakin da za su yi tafiyar tare a zaben shugaban kasa na shekarar 2023.
A siyasar Najeriya, zaben abokin tafiya yana taka babbar rawa wajen cin zabe. Duk da ya kamata tsohon mataimakin shugaban kasa ya zama mai taka tsan-tsan tare da wayau wajen zaben abokin tafiya a zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kasancewarsa musulmi dan arewa maso gabas, ana sa ran Atiku ya dauki abokin tafiya kirista daga yankin kudancin kasar; kudu maso gabas, kudu maso kudu ko kudu maso yamma.
Yayin da ake jiran Atiku ya bayyana ra'ayinsa, wadannan su ne jiga-jigan 'yan siyasar Najeriya da Legit.ng ta hasaso tsohon mataimakin shugaban kasar zai iya zaba:
1. Nyesom Wike
Wike wanda suka fafata a zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP na shugaban kasa, gwamnan jihar Ribas, ya tabbatar da kwarewar siyasarsa.
Duk da babban abokin hamayayya ne, Aminu Tambuwal ya janyewa Atiku, amma hakan bai hana Wike samun kuri'u 237 ba tare da zama wanda ke bi wa zakaran gwajin dafi a kuri'u a zaben fidda gwanin.
Gwamna Wike ya nuna yadda zai iya taimakawa Atiku wajen samun miliyoyin kuri'u daga yankin kudancin kasar a shekarar 2023.
Duk da kafin Atiku ya yi nasara, wani rahoto da jaridar Business Day ta nuni da yadda wasu majiyoyi suka bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya dauki gwamna Nyesom Wike a matsayin abokin tafiyarsa.
Dalili daya da yasa wata kila Atiku ba zai dauki Wike ba saboda yadda yake da wani irin tsatsauran ra'ayi. Idan ya zabi Wike a matsayin abokin tafiyarsa kuma su ka yi nasara, akwai yuwuwar 'yan Najeriya su kara ganin yadda tarihi zai maimaita kansa a kan irin zaman doya da manjan da su ka yi da tsakanin Atiku da uban gidansa, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
2. Ike Ekwdremadu
A lokacin da Atiku ya samu tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a shekarar 2019, mutane da dama sun yi zaton zai dauke shi a matsayin abokin tafiyarsa kafin daga bisani ya dauki tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, wanda a halin yanzu ya canza sheka daga PDP zuwa Labour party.
Yayin hangen karatowar zaben 2023, Ekwdremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma wanda ya dauki tsawon lokaci a majalisar tarayya, ya fito takara don zama gwamnan jihar Inugu.
Sai dai daga baya ya janye daga takarar zaben fidda gwanin saboda irin "Badakalar dake tsakaninsa da gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Inugu da shugabannin jam'iyyar PDP a kan fafutukar amsar tiketin tsayawa takarar gwamna a jam'iyyar a jihar."
Bayan janyewar da ya yi da wasan, akwai rahotanni da ke nuna cewa Ekweremadu zai iya canza sheka zuwa APC ko Labour party. Amma tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce har yanzu bai bar PDP ba.
Don tausar kudu maso gabas bayan shan kaye a zaben fidda gwanin a yankin, shugabannin PDP za su iya neman Atiku ya zabi Ekweremadu a matsayin abokin tafiyarsa.
3. Anyim
Shima wani babban dan siyasa ne daga kudu maso gabas wanda Atiku zai iya zaba a matsayin abokin tafiyarsa. Anyim, tsohon sakataran gwamnatin tarayya kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, shima ya nemi tiketin tsayawa takarar shugaban kasa a PDP wanda ya samu kuri'u 14. Da Anyim a matsayin abokin tafiyarsa, Atiku da PDP za su iya gamsar da kudu maso gabas su yi dandazo wajen kada musu kuri'u a shekarar 2023.
4. Ifeanyi Okowa
Yayin fara siyar da fom din takarar shugaban kasa a PDP, an samu jita-jitan cewa Ifeanyi Okowa zai shiga wasan.
Sai dai, gwamnan jihar Deltan bai nemi tiketin tsayawa takarar ba. A irin ficen da ya yi a kudancin PDP, Atiku zai iya daukansa a abokin tafiyarsa.
5. Udom Emmanuel
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom ya yi takara tare da Atiku, wanda ya tashi da kuri'u 38. Ya fi Bala kuri'u, takwaransa na Bauchi, kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Anyim.
Idan aka yi dubi da bauta wa PDP da ya yi, kasancewarsa matashi mai jini a jika, kuma dan siyasa mai kara yawan mabiya a kudu maso kudu, yadda PDP ke neman yadda za ta hucewa yankin kudu takaici, Atiku zai iya zabar gwamnan jihar Akwa Ibom a matsayin abokin tafiyarsa.
Asali: Legit.ng