Shugaban kasa: Nasarar Atiku babban kalubale ne ga APC a 2023 – Orji Kalu

Shugaban kasa: Nasarar Atiku babban kalubale ne ga APC a 2023 – Orji Kalu

  • Shugaban masu tsawatarwa na majalisar dattawa, Orji Kalu, ya magantu a kan lashe tikitin shugaban kasa na PDP da Atiku Abubakar ya yi
  • Orji Kalu ya ce idan har APC na so ta ci gaba da mulki a 2023, ya zama dole ta ajiye batun fitar da dan takara daga yankin kudu
  • Sanatan ya ce dole APC ta fitar da dan takara daga yankin arewa maso gabas domin su fafata da Atiku

Shugaban masu tsawatarwa na majalisar dattawa, Orji Kalu, ya bayyana cewa bayyanar Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party(PDP) yasa akwai bukatar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fitar da dan takara daga arewa idan har tana son ci gaba da mulki a 2023.

Kalu a cikin wata sanarwa da ya fitar jim kadan bayan ayyana Atiku a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin PDP na ranar Asabar, ya ce ya kamata APC ta dauki dan takara daga arewa maso gabas saboda daga yankin ne Atiku ya fito.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Atiku ya dauki wasu manyan alkawara, ya caccaki APC

Tsohon gwamnan na jihar Abia ya yi nuni ga zabar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan wanda ya fito daga jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya.

Lawan na daya daga cikin yan takarar shugaban kasa da ke son mallakar tikitin APC a zabe mai zuwa.

Shugaban kasa: Nasarar Atiku babban kalubale ne ga APC a 2023 – Orji Kalu
Shugaban kasa: Nasarar Atiku babban kalubale ne ga APC a 2023 – Orji Kalu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, tsohon gwamnan jihar Lagas, Bola Tinubu da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi na kan gaba wajen neman takarar kujerar a APC.

A cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na facebook, Mista Kalu ya ce:

“Ina taya PDP murna da ta zabi dan arewa maso gabas.
“Na san yan Najeriya sun ga abun da na gano a jiya. Ga jam’iyyarmu APC, babu damar magana kan yan takara daga kudu ba sai dai idan APC na so ta yi ritaya a siyasa ne.”

Kara karanta wannan

Na yi farin ciki da kasancewa dan takarar PDP a zaben 2023 – Atiku Abubakar

Sanata Kalu ya bukaci shugaban APC na kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da su tursasa APC daukar dan takararta daga yankin arewa maso gabas.
“Ina umurtan shugaban jam’iyyar na kasa da daukacin mambobin MWC da su dage kafafunsu sannan su mika tikitin shugaban kasa zuwa arewa maso gabas.
“Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana da yancin zabar magajinsa, kuma ina kira gare shi da ya zabi Sanata Ahmad Lawan a matsayin magajinsa.”

Sanatan ya kuma yi bayanin dalilin da yasa akwai bukatar Buhari ya tilastawa APC zabar dan takara daga yankin arewa maso gabas.

"A kowane yanayi na dimokuradiyya, shugabanni da gwamnoni suna goyon baya da kuma zabar magajin su. Ina kira ga Shugaba Buhari da ya zabo wanda zai gaje shi daga yankin Arewa maso Gabas kuma hakan zai kasance daidai da daidaiton da Kudu maso Gabas ke bukata."

Ya yi kira ga sauran yan takarar shugaban kasa na APC da su ajiye kudirinsu sannan su marawa Lawan baya.

Kara karanta wannan

2023: Da Yardar Allah Ni Da Kai Zamu Fafata a Zaɓen Shugaban Kasa, Tinubu Ya Taya Atiku Murna

Mista Kalu da kansa yana neman takarar shugaban kasa a APC. Daga bisani ya fita daga tseren sannan ya ayyana goyon bayansa ga Lawan.

Shugaban kasa a 2023: Atiku ya dauki wasu manyan alkawara, ya caccaki APC

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya dauki alkawarin hada kan kasar idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Atiku ya kuma dauki alkawarin tunkarar matsalar rashin tsaro da ya addabi kasar nan, jaridar Punch ta rahoto.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake bayar da jawabin amincewarsa bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin shugaban kasa na PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng