Cikakken sakamako: Yadda Atiku ya lallasa Wike, Saraki da sauransu wajen samun tikitin shugaban kasa na PDP

Cikakken sakamako: Yadda Atiku ya lallasa Wike, Saraki da sauransu wajen samun tikitin shugaban kasa na PDP

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya sake lashe zaben fidda gwanin shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Atiku ya samu kuri’u mafi yawa a zaben wanda ya gudana a filin wasa na MKO Abiola a Abuja a ranar Asabar, 28 ga watan Mayu.

Akalla deleget 767 ne suka kada kuri’u domin zartar da hukunci kan makomar masu takarar shugabancin kasar na jam’iyyar adawar da ke fafutukar mallakar tikitin jam’iyyar.

Cikakken sakamako: Yadda Atiku ya lallasa Wike, Saraki da sauransu wajen samun tikitin shugaban kasa na PDP
Cikakken sakamako: Yadda Atiku ya lallasa Wike, Saraki da sauransu wajen samun tikitin shugaban kasa na PDP Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Atiku ne ya bayyana a matsayin mai nasara da kuri’u 371, inda ya lallasa manyan yan takara irin su Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki wadanda suka samu kuri’u 237 da 70 kowannensu.

Ga cikakken sakamakon:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gudaji Kazaure Ya Sha Kaye a Zaɓen Fidda Gwanin APC a Jigawa, Akwai Yiwuwar Zai Koma NNPP

Atiku Abubakar: Kuri’u 371 (ya lashe zaben)

Nyesom Wike: kuri’u 70

Bukola Saraki: kuri’u: 70

Udom Emmanuel: kuri’u 38

Bala Mohammed: kuri’u 20

Pius Anyim: kuri’u 14

Olivia Tariela: kuri’a 1

Gaba daya jimillar kuri’u: 763

Kuri’u masu inganci: 751

Kuri’u da aka soke: 12

Zaben 2023: Jam'iyyar PDP ta fi APC tsoron Allah - Gwamna Fintiri

A wani labarin, Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya yi imani da cewa PDP ita ce mafita ga 'yan Najeriya a kan jam'iyya mai mulki (APC) kuma PDP ta fi APC tsoron Allah. Gwamnan ya zanta da Channels Television a game da gangamin zaben PDP na kasa, wanda ake gabatarwa a ranar Asabar a Abuja.

Yayin da ya amince da cewa jam'iyyar ta yi kuskure a baya, amma duk da haka ita PDP ta zarcewa APC.

Yayi imani da cewa, da 'yan takara masu nagarta da suka zagaye PDP tare da shirin da jam'iyyar tayi, APC ba za ta zo kusa da jam'iyyarsa ba.

Kara karanta wannan

Tsohon Hadiman Buhari da ke takara a Kano ya fice, ‘yan daba sun cika wajen zaben APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng