EFCC ta bayyana dalilinta na yin dirar mikiya a filin zaben fidda gwanin PDP na kasa
- Jami'an hukumar EFCC sun yi dirar mikiya wurin zaben fidda'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP don lura da yadda ake shakata wakilin jam'iyyar dukiya
- Kamar yadda hukumar ta bayyana, ta yi hakan ne don kawo karshen toshiyar baki da ake bai wa wakilan jam'iyyar adawa a zaben fidda gwanin a MKO Abiola Stadium dake Abuja
- Hakan yazo ne bayan samun rahoto da hukumar ta yi a kan yadda ake zargin ana siyar da kuri'u tare da bada cin hanci ga wakilan jam'iyyar
FCT, Abuja - Hukumar yaki da almundahana tare hana yi wa tattalin arzirkin kasa zagon kasa (EFCC), ta bayyana yadda jami'anta suka yi dirar mikiya wajen da ake gudanar da zaben fidda 'dan takarar shugaban kasa na babbar jam'iyyar adawa.
Ana taron ne a Moshood Kashimawo Abiola National Stadium a Abuja. Jami'an sun bayyana ne don sa ido a kan yadda ake shakara wa wakilan jam'iyya kudi da tare da almubazzaranci.
Zaben fidda gwanin PDP: Har yanzu akwai damar fitar da dan takarar maslaha – Shugaban kwamitin amintattu
Kakakin hukumar yaki da almundahana, Wilson Uwujaren, wanda ya zanta da Punch a yammacin Lahadi ya ce:
"A halin yanzu, wakilanmu na wurin zaben fidda 'dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a MKO Abiola Stadium don sa ido a kan yadda ake gudanar da zaben, musamman don kula da yadda ake bada toshiyar baki ga wakilan jam'iyyar da sauran almubazzaranci da ake a dukiya."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da farko dai, TheCable ta ruwaito yadda jami'an EFCC suka yi dirar mikiya wajen zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP a Abuja bayan samun wani rahoto da ake zargin ana siyar da kuri'u tare da bada toshiyar baki ga wakilan jam'iyyar a wurin da ake gabatar da zaben.
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng