Zaben fidda gwanin PDP: Har yanzu akwai damar fitar da dan takarar maslaha – Shugaban kwamitin amintattu

Zaben fidda gwanin PDP: Har yanzu akwai damar fitar da dan takarar maslaha – Shugaban kwamitin amintattu

  • Yayin da ake tsaka da gudanar da babban taron PDP, akwai yiwuwar jam’iyyar ta yi amfani da tsarin maslaha wajen fitar da dan takararta na shugaban kasa
  • Wannan shine jawabin da shugaban kwamitin amintattu na PDP, Walid Jibril, ya yi a wajen zaben fidda gwanin a ranar Asabar, 28 ga watan Mayu
  • Jibril ya ce akwai damar fitar da dan takarar maslaha duk da cewar PDP ta yi watsi da tsarin karba-karba

Abuja - Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Sanata Walid Jibril, ya ce duk da cewar jam’iyyar ta yi watsi da tsarin karba-karba, har yanzu akwai damar yin maslaha.

Walid ya fada ma Daily Trust a wajen babban taron jam’iyyar cewa dukkanin yan takarar sun fahimci matsayin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Ba mu dage zaben fidda dan takarar shugaban kasa ba - PDP

Zaben fidda gwanin PDP: Har yanzu akwai damar yin maslaha – Shugaban kwamitin amintattu
Zaben fidda gwanin PDP: Har yanzu akwai damar yin maslaha – Shugaban kwamitin amintattu Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Ya kuma bayyana cewa taron zai samar da Shugaban kasar Najeriya a 2023.

Walid ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Wannan babban taron zai sanar da yan Najeriya da yan PDP cewa shugaban kasar Najeriya na gaba zai fito ne daga PDP.
“Wannan ne dalilin da yasa kuka ga wannan wajen ya cika da harkoki, maza da mata sun zo nan ne saboda shugaban kasar Najeriya na gaba zai bayyana a nan.
“Duk wanda ya bayyana a yau imma daga arewa, kudu maso kudu, kudu maso yamma ko kudu maso gabas ya shirya zama shugaban kasar nan.
“Kun riga kun san cewa babu tsarin karba-karba, amma akwai damar maslaha.”

Mun ji yadda wasu yan takara suka yarda su janyewa junansu.

Tikitin shugaban kasa na PDP: Ina addu’a Allah yasa Wike ya kai labari – Okezie Ikpeazu

Kara karanta wannan

Batun fitar da dan takarar maslaha ya rushe: Atiku, Saraki da sauran yan takarar PDP sun ce sai an fafata

A wani labarin, mun kawo cewa yayin da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta fara babban taronta na kasa a yau Asabar, 28 ga watan Mayu, gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya bayyana cewa yana son gwamnan jihar Abia, Nyesom Wike ya kai labari.

Ikpeazu ya bayyana haka ne a wajen zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, jaridar Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng