Batun fitar da dan takarar maslaha ya rushe: Atiku, Saraki da sauran yan takarar PDP sun ce sai an fafata
- Har zuwa yau Asabar, 28 ga watan Mayu da ake gudanar da zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP, ba a yi nasarar tsayar da dan takarar maslaha daga arewa ba
- Manyan masu takarar kujerar a yankin da suka hada da Atiku, Tambuwal, Saraki da Bala Mohammed sun ce lallai sai dai kowa ya gwada sa'arsa
- Babban dan kasuwa, Mohammed Hayatu-Deen ne kadai ya bi shawarar dattawan yankin wajen janyewa daga tsere
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Wani taro da aka kawo karshen shi a safiyar yau Asabar tsakanin manyan shugabannin PDP daga arewa ya tashi ba tare da anyi nasarar tsayar da dan takarar maslaha ba, Daily Trust ta rahoto.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, Gwamna Aminu Tambuwal da Gwamna Bala Mohammed sun yi biris da bukatar dattawan yankin na janyewa da marawa mutum daya a cikinsu baya.
Zaben fidda dan takarar PDP: An gano fostocin Hayatu-Deen baje a wajen taron duk da janyewa daga tseren
Shahararren dan kasuwa Mohammed Hayatu-Deen ne kadai ya yarda ya janye daga tseren.
An tattaro cewa shugabannin jam’iyyar na kokarin ganin manyan yan takarar sun fito da hadin kai don fuskantar Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas wajen kwace tikitin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wata majiya da ke sane da ganawar da aka yi cikin dare ta ce:
“Da yawa daga cikinsu basu yarda cewa Wike zai iya lashe babban zaben ba amma ga dukkan alamu zai iya yin nasara idan yan takarar arewa basu dinke barakarsu ba.”
A halin da ake ciki, deleget da jami’an jam’iyyar sun fara tururuwa a dakin taro na MKO Abiola, wajen taron fidda dan takarar shugaban kasa na PDP.
Zaben fidda dan takarar PDP: An gano fostocin Hayatu-Deen baje a wajen taron duk da janyewa daga tseren
A gefe guda, mun ji cewa an gano fostocin mai takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Mohammed Hayatu-Deen, baje a wurare masu muhimmanci a filin babban taron jam’iyyar duk da cewar ya sanar da janyewarsa daga tseren.
Daily Trust ta rahoto cewa an baje kolin hotunan shahararren dan kasuwar a manyan wurare a filin wasa na Moshood Abiola, wajen zaben fidda gwanin jam’iyyar adawar tare da sauran manyan yan takara.
Hakazalika a gano fostocin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, na gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, Bala Mohammed na jihar Bauchi da tsohon shugaban majalisar dattawa, Anyim Pius Anyim.
Asali: Legit.ng