Halin da Atiku, Saraki, Tambuwal, da Wike suke ciki a wajen zaben zama ‘dan takaran PDP
- Tsakanin ranar Asabar da Lahadin nan ne jam’iyyar PDP za ta gudanar da zaben tsaida gwaninta
- A filin wasan Moshood Abiola na Abuja za a gudanar da zaben da manyan ‘yan siyasa za su gwabza
- Masu neman tikiti sun kunshi: Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Nyesom Wike da Aminu Tambuwal
Premium Times ta yi bincike da hasashen yadda wannan zaben na tsaida gwani zai kasance:
1. Atiku Abubakar
Wannan ne karo na shida da Atiku Abubakar yake neman shugaban kasa. Tsohon mataimakin shugaban kasar ba sabon shiga-bane, ya yi takara a 2019.
Wazirin Adamawa yana da karfi a irinsu: Adamawa, Taraba, Gombe da Borno. Baya ga haka yana cikin manyan Attajirin kasar nan da ke da kudin cin zabe.
Ba dole ba ne Atiku ya samu kuri’u sosai a yankin kudu maso gabas musamman bayan raba jiha da Peter Obi da kuma ganin cewa daga yankin Arewa ya fito.
Baya ga haka, ana tunanin cewa a shekara 75, Atiku ya yi tsufa sosai, amma buge shi sai an shirya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
2. Aminu Tambuwal
Wannan ne karo na biyu da Aminu Waziri Tambuwal zai nemi takarar shugaban kasa, duk yana kan kujerar gwamna. Shi ya zo na biyu a zaben PDP na 2018.
A yau Aminu Waziri Tambuwal ne kadai ‘dan takaran PDP daga Arewa maso yamma – inda ya fi ko ina yawan kuri’u, sai dai kuma yankin ne ke kan mulki.
Jaridar ta ce Tambuwal yana da mutane a Gombe, Ondo, Benue da Imo, amma ya rasa goyon bayan Nyesom Wike wanda ya ba shi gudumuwa a zaben 2019.
3. Bukola Saraki
Wani fitaccen mai neman takara a PDP shi ne Bukola Saraki. Kamar Tambuwal, shi ma ya taba rike kujerar gwamnan jiha da na shugaban majalisar dattawa.
A matsayinsa na mutumin jihar Kwara, Bukola Saraki zai amfana da kuri’u 130 na Arewa maso tsakiya, ko da Nyesom Wike yana tare da irinsu Samuel Ortom.
Saraki yana cikin masu kananan shekaru da kuma tafiya da zamani, sai dai yana cikin wadanda suka fice daga PDP, su ka shiga jam’iyyar APC kafin zaben 2015.
4. Nyesom Wike
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya fito neman takarar shugaban kasa a PDP gadan-gadan, ya na ikirarin bai ci amanar jam’iyya a lokacin da aka fadi zabe ba.
Ana tunanin Nyesom Wike yana da kudin da zai iya kashewa wajen samun tikiti, sannan ya sha gaban duk masu harin zama ‘dan takara daga kaf yankin Kudu.
Alamu na nuna zai iya samun kuri’un PDP na Neja-Delta, kasashen Ibo da jihohin Benuwai da Oyo. Saboda yanayin babatunsa, zai yi wahala ya dace a Arewa.
5. Pius Anyim
Anyim Pius Anyim yana cikin wadanda suka fara nuna sha’awar takara a PDP. Sanata Anyim ya rike sakataren gwamnati da shugaban majalisar dattawa a baya.
Sai dai duk da irin kwarewarsa wajen aiki, da alama abu inda Anyim Pius Anyim zai kai labari a zaben yau, sai yankin da ya fito na kudu maso gabashin Najeriya.
Tsohon shugaban majalisar dattawan yana cikin masu hakikance a ba ‘Dan kudu takara a zabe mai zuwa, sannan babu mai shakkar amanarsa na zama a jam’iyya.
6. Bala Mohammed
Bala Mohammed ya dage kan batun neman takarar shugaban kasa duk da bai kammala wa’adinsa na gwamna ba, yadda Aminu Tambuwal ya yi a 2018.
Takarar Gwamna Bala Mohammed ta samu kwarin gwiwa bayan da dattawan Arewa suka ayyana shi da Bukola Saraki a matsayin wadanda suke marawa baya.
Ana tunani idan tsohon Ministan bai hakura da neman takarar ba, zai tashi da kuri’un jihar Bauchi. Har yanzu ba a fahimci inda Kauran Bauchi ya sa gaba ba.
7. Sauran ‘yan takara
Ragowar masu neman takara a PDP sun hada da Ayo Fayose wanda yayi gwamna a Ekiti, da farko yana tare da Nyesom Wike, amma daga baya sai ya shiga takaran.
Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel ya na neman tikiti, amma ana tunanin zai janye, ya marawa wani baya, babu mamaki a ji ya na tare da Nyesom Wike.
A cikin ‘yan takarar akwai; Dele Momodu, Tariela Oliver, Sam Ohabunwa, Charles Ugwu da Chikwendu Kalu, duk zai yi wahala wadannan su je da nisa a yau.
Asali: Legit.ng