Zaɓen Fidda Gwanin APC: Da Ƙyar Na Sha, Dole Na Tsere Don Kada a Kashe Ni, In Ji Ɗan Majalisa

Zaɓen Fidda Gwanin APC: Da Ƙyar Na Sha, Dole Na Tsere Don Kada a Kashe Ni, In Ji Ɗan Majalisa

  • Dan majalisa mai wakiltar mazabar Akure ta Kudu da Akure ta Arewa a Jihar Ondo, kuma dan takarar APC, Mayiwa Lawson Alade ya sanar da yadda ya sha da kyar a hannun mahara
  • Hakan ya sa Lawsonya bukaci a rushe zaben fidda gwanin da aka yi a Akure, babban birnin jihar, inda ya sanar da manema labarai cewa ‘yan bangar siyasa sun kai farmaki ana gab da kammala zaben
  • Ya ce sun hargitsa wurin yayin da ake kirga kuri’u, sannan sun dauke wakilinsa inda aka tsince shi jiki duk rauni, sun lakada masa duka, shi kuma dan takarar ya sha da kyar

Ondo - Mayiwa Lawson Alade, dan majalisa mai wakiltar Akure ta Kudu da kuma Akure da Arewa a Jihar Ondo, kuma dan takarar APC a zaben fidda gwani, ya labarta yadda ya sha da kyar yayin da aka yi yinkurin halaka shi ana tsaka da zaben fidda gwanin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Tsohon Hadiman Buhari da ke takara a Kano ya fice, ‘yan daba sun cika wajen zaben APC

Hakan ya sa Lawson ya nemi jam’iyyar ta rushe zaben kuma ta wofantar da shi kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Dan Majalisar APC Ya Tsere Daga Wurin Zaben Fidda Gwani Don Gudun Kada a Bindige Shi
Zaben Fidda Gwanin APC: Dole ta sa na gudu kada a kashe ni, Dan Majalisar APC. Hoto: Vanguard.
Asali: Twitter

Ya sanar da manema labarai da tsakar daren jiya cewa ana tsaka da zaben, ‘yan bangar siyasa su ka kai farmaki bayan sun ga ya na gab da cin nasara.

Ya ce matasa sun shiga damuwa akan yadda ‘yan bangar su ka lalata zaben

A cewarsa bisa ruwayar Vanguard:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Kowa ya shiga damuwa akan zaben Akure, ko wanne matashi na Jihar Ondo, musamman na mazabar Akure ta Arewa da Kudu ta tarayya ya damu akan yadda ‘yan bangar siyasa su ka fado wurin zaben ana tsaka da kirga kuri’u muna ta farin ciki don nasara ta na harararmu inda su ka lalata komai.
“Kamar yadda ku ka gani, an zane wakilina sannan an gdauke shi, sai dai mu ka ganshi da raunuka, har ni ba su bari ba. Dakyar na tsere don harsashi ya kusa samu na.

Kara karanta wannan

Kano: An Yi Yunƙurin Kashe Ni Yayin Zaɓen Fidda Gwani, Ban Yarda Da Zaɓen Ba, Ɗan Takarar Gwamnan APC

“Maganar gaskiya ba a yi zabe ba, kuma muna fatan za a sauya zaben. Tun daga farko ‘yan bangar su ka fara kawo farmaki, bayan wani dan takara ya koka akan yadda bai ga sunansa ba a takardar zaben. A fusace ya ke, hakan ya sa sai da aka kusa kammala komai, sai ‘yan bangar siyasar su ka lalata komai.”

Ya bai wa masoyansa hakuri akan su kwantar da hankulan su

Ya ci gaba da cewa idan aka duba abinda ya faru, babu wani zaben da aka yi, kuma su na fatan shugabannin jam’iyyar za su sauya wata rana don a gabatar da zaben gaskiya da gaskiya.

Ya ce mutanensa su na matukar son sa, watanninsa biyu kenan a majalisa, hakan ya sa ya ga dacewar ya koma.

Ya bai wa masoyansa hakuri, inda ya ce sun kwantar da hankulansu, Ubangiji ya na tare da su.

Kano: An Yi Yunƙurin Kashe Ni Yayin Zaɓen Fidda Gwani, Ban Yarda Da Zaɓen Ba, Ɗan Takarar Gwamnan APC

Kara karanta wannan

Sokoto: Ƴan Takarar APC Sun Fice Daga Wurin Zaɓen Fidda Gwani a Fusace Bayan Ɗaukewar Wutar Lantarki

A wani rahoton, dan takarar gwamna karkashin inuwar jam’iyyar APC, Sha’aban Sharada, ya bayyana dalilinsa na barin inda ake zaben fidda gwanin jam’iyyar APC, kuma ya kalubalanci sakamakon zaben.

Sharada ne dan takara daya da ya nuna rashin amincewarsa akan gabatar da mataimakin gwamnan jihar, Nasir Gawuna, a matsayin dan takarar gwamna a farkon watan Mayu, rahoton The Cable.

A wata takarda wacce Daily Nigerian ta saki ranar Juma’a, Sharada ya ce dakyar shi da wasu mabiyansa su ka sha daga harin da aka kai musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164