Abubuwan da ya kamata ka sani gane da jiga-jigan siyasan Adamawa 5 da Aishatu Binani ta tikar

Abubuwan da ya kamata ka sani gane da jiga-jigan siyasan Adamawa 5 da Aishatu Binani ta tikar

Tuni kun ji cewa Sanata Aishatu Binani ta lallasa gardawa biyar a zaben fidda gwanin yan takaran gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Adamawa.

Binani ta zama mace ta farko da ta lashe zaben fidda gwanin APC a jihar Adamawa.

Shugaban kwamitin zaben, Gamba Lawan, yayin sanar da sakamakon ya bayyana cewa Binani ta samu kuri'u 430.

Legit ta tattaro muku wasu abubuwa da ya kamata ku sani game da jiga-jigan siyasa mazaje 5 da Aisha Binani ta kayar a zaben bana:

1. Umaru Jibrilla Bindow

- Sanata, mamban majalisar dattijai (2011–2015)

- Tsohon Gwamnan jihar Adamawa (2015-2019)

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Babban dan kasuwa kuma jigon APC

Kara karanta wannan

Karin bayani: APC ta sanar da wanda ya lashe zaben fidda gwanin gwamna a bauchi

Bindow
Fuskokin jiga-jigan siyasan Adamawa 5 da Aishatu Dahiru Binani ta tikar Hoto: Jibrilla Bindow
Asali: Facebook

2. Nuhu Ribadu

- Tsohon mataimakin Sifeto Janar na yan sanda

- Tsohon shugaban hukumar bibiyan kudin shigan man fetur

- Tsohon Shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC)

- Tsohon dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin ACN a zaben 2011

- Wanda ya zo na uku a zaben gwamnan jihar Adamawa a 2019

Fuskokin jiga-jigan siyasan Adamawa 5 da Aishatu Dahiru Binani ta tikar
Fuskokin jiga-jigan siyasan Adamawa 5 da Aishatu Dahiru Binani ta tikar Hoto
Asali: UGC

3. AbdulRazaq Namdas

- Tsohon Sakataren yada labarai na tsohon gwamnan Adamawa, Boni Haruna

- Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jada/Ganye/MayoBelwa/Toungo (2015-)

- Tsohon mai magana da yawun majalisar wakilai (2015-2019)

Fuskokin jiga-jigan siyasan Adamawa 5 da Aishatu Dahiru Binani ta tikar
Fuskokin jiga-jigan siyasan Adamawa 5 da Aishatu Dahiru Binani ta tikar Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

4. Umar Mustapha Madawaki

- Tsohon Mukaddas Adamawa

- Jigon APC a jihar Adamawa

Mustapha
Fuskokin jiga-jigan siyasan Adamawa 5 da Aishatu Dahiru Binani ta tikar
Asali: UGC

5. Wafari Theman

- Shugaban Mentors International Conferences and Seminars

- Masanin ilmin magunguna

Wafari
Fuskokin jiga-jigan siyasan Adamawa 5 da Aishatu Dahiru Binani ta tikar Hoto: tgnews.com.ng/tag/wafari-theman
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel