An yanka ta tashi: Kotu ta kori dan takarar gwamna daga APC bayan lashe zaben fidda gwani

An yanka ta tashi: Kotu ta kori dan takarar gwamna daga APC bayan lashe zaben fidda gwani

A kasa da sa’o’i biyu bayan ya zama dan takarar gwamna a APC a Abia, wata babbar kotun jihar Abia da ke da zama a Umuahia, ta tabbatar da dakatar da Cif Ikechi Emenike daga jam’iyyar APC, kamar yadda 'yan unguwarsu suka nema.

Kotun karkashin jagorancin Hon. Justice A.O. Chijioke a hukuncin da ya yanke, ya ce dakatar da Emenike ya hana shi duk wasu damammakin zama mamban jam'iyyar kamar yadda kundin tsarin mulkin APC ya tanada.

Dan takarar APC ya rasa tikitin takara saboda rikicin kotu
An yanka ta tashi: Kotu ta kori dan takarar gwamna daga APC bayan lashe zaben fidda gwani | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewar hukuncin kotun:

"Manufar wannan hukunci shine Cif Ikechi Emenike bai cancanci shiga da/ko tsayawa takara a zaben fidda gwani na jam'iyyar APC da ke gudana a jihar Abia ba har sai an cire hukuncin a gefe ko kuma a soke hukuncin da aka yanke."

Kotun ta hana Emenike bayyana kansa a matsayin halaltaccen dan jam’iyyar APC, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An samu matsala: 'Yan bindiga sun harbe deliget 3 na zaben gwamnan PDP a jihar Arewa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka kuma ta hana APC amincewa ko mu’amala da Emenike a matsayin mambanta yayin da dakatarwar ke ci gaba da aiki akansa.

Mambobin jam’iyyar APC reshen jihar Abia mutum uku ne suka shigar da karar suna kalubalantar matsayin Cif Ikechi Emeinike a APC, duk kuwa da dakatar da shi da jam'iyyar ta yi, saboda wasu ayyukan da suka saba ka'ida.

Mutanen uku da ke cikin karar sun samu wakilcin Anaga Kalu Anaga Esq, yayin da Cif Ikechi Emenike da APC suka samu wakilcin Vitalis C.Nwankwo Esq.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel