Shirin 2023: Jerin jihohi 22 da 'yan siyasan da suka samu tikitin takarar gwamna a PDP

Shirin 2023: Jerin jihohi 22 da 'yan siyasan da suka samu tikitin takarar gwamna a PDP

A ranar Labara 25 ga watan Mayu ne rahotanni suka fara karade Najeriya na wadanda suka lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar adawa ta PDP a shirin babban zaben 2023, lamarin da ya ke ci gaba da daukar hankali.

Yayin da rahotannin suke a warwatse, Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin 'yan takarar da suka tsallake, kana suka samu tikitin yin takarar gwamna a jihohinsu a karkashin inuwar jam'iyyar ta PDP.

Duk da cewa akwai jihohin da aka samu tsaiko, kamar yadda rahotanni suka fada, mun tattaro adadin wadanda aka kammala da kuma jihohin da har yanzu ba a samu sakamako ba.

Yadda taron zaben fidda gwanin PDP ya gudana, da wadanda suka lashe zaben fidda gwani
Shirin 2023: Jerin wadanda suka lashe zaben fidda gwani na tikitin gwamnan PDP | Hoto: vanguardngr.com

Wadanda suka lashe zaben fidda gwanin gwamna na PDP

Ga jerin kamar haka:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

PDP ta tsaida ‘Yan takarar Gwamna 2 a jihar Kano, ‘Ya ‘yan Wali da Abacha sun samu tikiti

  1. Abia - Farfesa Uche Ikenna
  2. Adamawa - Ahmadu Finitiri
  3. Akwa Ibom - Umo Eno
  4. Anambra - An yi zabe tun a watan Nuwamban 2021
  5. Bauchi - Ibrahim Kashim
  6. Benue - Titus Uba
  7. Borno - Mohammed Jajari
  8. Cross Rivers - Sandy Onor
  9. Enugu - Peter Mba
  10. Delta - Rt Hon Sheriff Oborevwori
  11. Gombe - Muhammad Jibril Dan Barde
  12. Jigawa - Mustapha Suke Lamido
  13. Kaduna - Isa Muhammad Ashiru
  14. Kano - Muhammad Abacha
  15. Lagos - Olajide Adediran (Jandor)
  16. Nasarawa - David Ombugadu
  17. Ogun - Segun Sowunmi
  18. Oyo - Seyi Makinde
  19. Plateau - Caleb Mutfwang
  20. Rivers - Siminaliayi Fubara
  21. Sokoto - Sa'idu Umar
  22. Taraba - Agbu Kefas
  23. Yobe - Shariff Abdullahi
  24. Zamfara - Dauda Lawal

Jihohin da suka saura:

  1. Bayelsa -
  2. Ebonyi -
  3. Edo -
  4. Ekiti -
  5. Imo -
  6. Katsina -
  7. Kebbi -
  8. Kogi -
  9. Kwara -
  10. Niger -
  11. Ondo -
  12. Osun -

Kara karanta wannan

Harkallar Kwaya: Bayan tsallake kisa a magarkama, Kyari da abokansa sun bayyana a kotu

An gano dalilin da yasa APC ta gaza tantance masu takarar shugabancin kasa a jam'iyyar

A wani labarin, akasin rahotannin da ke yawo kan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na cewa ya fita daga jerin masu takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC saboda bai mayar da fom din takararsa ba, Vanguard ta tattaro cewa yana nan daram cikin 'yan takara. Majiyoyi sun ce ya mayar da fom din har ofishin jam'iyyar.

Sai dai shugabannin jam'iyyar sun gaza tabbatar da cewa ko ya bar jam'iyyar PDP ko kuma yana nan har yanzu.

Wasu daga cikin shugabannin PDP da suka samu jagorancin Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe a farkon makon nan sun gana da Jonathan domin shawo kansa kan ya zauna a PDP kuma ya halarci taronsu da za a yi a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel