Yanzun Nan: Tsohon Minista Labaran Maku ya janye daga zaɓen fidda gwanin PDP a Nasarawa

Yanzun Nan: Tsohon Minista Labaran Maku ya janye daga zaɓen fidda gwanin PDP a Nasarawa

  • Tsohon minista a Najeriya, Labaran Maku, ya sanar da janye wa daga takarar gwamnan Nasarawa bayan fara zaɓen fidda gwanin PDP
  • Maku ya ce bayan dogon nazari da kuma shawari da iyalansa da makusantansa na siyasa ya ɗauki matakin na janye wa
  • A cewarsa nan gaba kaɗan zai bayyana wa duniya manyan dalilansa na jingine takarar zama gwamnan Nasarawa

Nasarawa - Tsohon Ministan yaɗa labarai, Labaran Maku, ya sanar da janye wa daga tseren neman tikicin PDP a zaɓen gwamnan jihar Nasarawa bayan an fara zaɓen fidda gwani.

Vanguard ta rahoto cewa Maku ya ce bayan faɗaɗa neman shawari daga abokansa da makusanta, ya yanke shawarin janye wa daga nema takarar gwamnan.

Tsohon minista, Labaran Maku.
Yanzun Nan: Tsohon Minista Labaran Maku ya janye daga zaɓen fidda gwanin PDP a Nasarawa Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Game da ko yana da wasu dalilai da suka ja hankalinsa ya ɗauki wannan matakin, Maku ya ƙara da cewa shi kaɗai ya san babban dalilin janyewarsa.

Kara karanta wannan

Sanata da wasu yan takara 6 sun janye daga zaben fidda gwanin PDP, jerin sunayen su

Tsohon ministan ya ce zai bayyana wa duniya manyan dalilansa na janyewa daga takarar gwamnan Nasarawa nan gaba kaɗan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa Labaran Maku ya ce:

"Na yanke matakin janye wa daga takara ne bayan faɗaɗa neman shawari daga iyalaina, abokanan siyasa na da sauran ma su ruwa da tsaki."
"Hakan ra'ayi na ne, matakan gudanar da zaɓen fidda gwani na jam'iyyar PDP na cigaba da tafiya a jihar Nasarawa."

A ranar Laraban nan da muke ciki, babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa PDP ta tsara aiwatar da zaben fidda yan takararta na gwamna a babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Zaɓen na cigaba da gudana a mafi yawan jihohin Najeriya yayin da wasu jihohin kamar Neja rikici ya sa aka ɗauki matakin ɗage wa, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Ɗan takarar gwamna a PDP ya janye daga zaɓen fidda gwani, ya fara shirin komawa APC

A wani labarin na daban kuma Yan majalisar wakilai ta tarayya guda 6 sun yi amai sun lashe, sun koma PDP daga APC

Yayin da jam'iyyar APC ke ganin ta shawo kan rikicin da ya addabeta a Zamfara, wata sabuwar ɓaraka ta sake barkewa.

Yan majalisar wakilan tarayya guda 6 da suka bi gwamna zuwa APC sun lashe aman su, sun sake komawa jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262