Da dumi-dumi: Bayan janyewa daga takarar shugaban kasa, Peter Obi ya fice daga PDP
2 - tsawon mintuna
Mai neman takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Peter Obi, ya fice daga jam’iyyar, jaridar The Nation ta rahoto.
Har zuwa lokacin da ya sauya sheka, Obi wanda ya kasance tsohon gwamnan jahar Anambra, yana daya daga cikin yan takara 15 da ke neman tikitin babbar jam’iyyar adawa ta kasar.
Obi ya sanar da sauya shekar tasa a cikin wata wasika da ya fitar mai kwanan wata Talata, 24 ga watan Maris dauke da sa hannunsa, TVC News ta rahoto.
An gabatarwa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu, da wasikar sauya shekar tasa.
Wasikar ta ce:
“Na rubuto maka wannan wasika ne domin in sanar da kai batun murabus dina daga jam’iyyar PDP, wanda aka mikawa shugaban gundumar Agulu 2. Karamar hukumar Anaocha, Anambar, wanda zai fara aiki daga Juma’a 20 ga watan Mayun 2022. Saboda haka, da wannan wasikar na ke sanar da ku janyewana daga zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP.
“Babban abin alfahari ne yadda muka ba da gudunmawarmu a kokarin gina kasa ta hanyar jam’iyyarmu. Abun takaici, lamuran da ke faruwa a jam’iyyarmu a baya-bayan nan ya sa ba zan iya ci gaba da kasancewa cikin wannan tafiya da bayar da gudunmawa mai muhimmanci ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Matsalolin kasarmu na da zurfi kuma suna bukatar kowannenmu ya sadaukar da abubuwa sosai don ceto kasarmu. Jajircewana don ceto Najeriya yana nan daram, koda kuwa hanyar ta sha banban.
“Ina fatan mika godiyata gare ka a kan alheri da shugabancinka. Ina maka fatan alkhairi a wajen aikin kasa.”
Asali: Legit.ng