Zaben Fidda Gwanin PDP: Bidiyon Ƙannen Fayose Suna Tiƙa Rawa Da Waƙar Zolayar Dino Melaye
- Bisa ga duka alamu Dino Melaye ya saduda bayan an lallasa shi a zaben fidda gwani na yankin Kogi ta Yamma
- Dino, ya amince da kayensa inda ya wallafa rubutu yana taya Teeja Yusuf murnar nasarar kuma ya gode wa wakilai da suka zabe shi
- Sai dai ya bayyana cewa taron dangi da aka yi masa ne yasa ya rasa tikitin kujerar inda ya samu kuri'u 99 shi kuma Yusuf ya samu 163
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Masu iya magana suna cewa duniya tamkar rawar yan mata ne, idan yau kai ne a gaba gobe kuma wani ne zai shige gabanka.
Wannan darasin ita ce ta faru da Sanata Dino Melaye bayan ya sha kaye a zaben fidda gwani na kujerar sanatan yankin Kogi West na PDP, hannun Teejay Yusuf, mamba mai wakiltar Kogi a Majalisar Wakilai a ranar Talata 24 ga watan Mayu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A wani bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta wacce Legit.ng ta yi karo da shi, an ga kanen tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose suna tika rawa kan kayen da Sanata Melaye ya sha.
An gano mutanen biyu suna rawa da juyi sallon yadda Melaye ya saba yi a bidiyonsa a baya suna rera waka.
"Dino, ka sha kaye, Dino! Ka sha kaye, ka sha kaye, Dino! ka sha kaye, Dino, ka rabu da majalisar dattawa kenan kwata-kwata," in ji su.
2023: Tsohuwar Matar Shugaban APC Na Kasa Ta Siya Fom Din Takarar Gwamna a Nasarawa
A wani rahoton, Fatima Abdullahi, tsohuwar matar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ta siya fom din takarar gwamnan Jihar Nasarawa, The Sun ta rahoto.
Za ta tsaya takarar ne don a yi zaben fidda gwani na jihar nan da wata daya, The Punch ta ruwaito.
Yayin da ta ke bayani bayan tuntubar shugabannin APC a ofishin jam’iyyar da ke Lafia, ranar Juma’a, Fatima ta ce ta tsaya takarar ne don gyara akan kura-kuran da wannan mulkin ya yi.
A cewarta, Jihar Nasarawa tana bukatar shugaba mai hangen nesa da kuma jajircewa don ciyar da jihar gaba.
Asali: Legit.ng